An daura auren zaurawa sama da 1,000 a Kano

An daura auren zaurawa sama da 1,000 a Kano

-Gwamna Ganduje ya jagorancin daurin auren zaurawa sama da 150,20 a Kano

-A yau ne aka yi taron daurawa zaurawa sama da 1,502. aure a jihar Kano a karkashin hukumar Hisbah

-Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Mai martaba sarkin Kano ne suka jagoranci taron daurin auren da aka yi babban masallacin Juma'a na cikin birnin Kano da kuma kananan hukumomi na 44

An daura auren zaurawa sama da 1,000 a Kano
Gwamna Ganduje da mai martaba sarkin Kano

A yau ne 26 ga watan Fabarairu shekarar 2017 aka daurawa zaurawa sama da 1,000 aure a jihar Kano a karkashin hukumar Hisabah.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi na II ne su ka jagoranci daurin auren da aka yi babban masallachin Juma'a na mai Martaba Sarki da ke cikin birni.

An dai karkasa daurin auren ne zuwa manyan masallatan juma'a 4 na cikin kwaryar birnin inda mataimakin gwamna Hafiza Abubakar, da kakakin majalisar dokokin jihar, da kuma shugaban hukumar Hisbah su ka jagoranta.

An kuma karkasa sauran wurararen daurin sauran zuwa kananan hukumomi 44 na jihar a inda aka gudanar a masallatan Juma'ar shalkwatar kananan hukumomin.

An kuma gudanar walima a gidan gwamnatin jihar Kano inda malamai suka yiwa ma'auratan liyafa tare da wa'azi kan muhimmancin aure.

Ga hotunan daurin auren da aka yi da babban masallacin Juma'a na cikin birni

Gwamnatin jihar ta shirya bayar da sadakin Naira 20,000 sadaki ga amaren tare da kayan daki

An daura auren zaurawa sama da 1,000 a Kano
An daura auren zaurawa sama da 1,000 a Kano

An daura auren zaurawa sama da 1,000 a Kano
An daura auren zaurawa sama da 1,000 a Kano

An daura auren zaurawa sama da 1,000 a Kano
Mai martaba Sarkin Kano da Gwamna da kuma waliyan amaren a yayin daurin auren

An daura auren zaurawa sama da 1,000 a Kano
Wasu daga cikin angwayen tare da Limamin Kano Farfsesa Sani Zaraddeen a taron daurin auren

An daura auren zaurawa sama da 1,000 a Kano
Jami'in Hisbah dauke da kudin sadakin ma'auratan da za a ba waliyan amare

An daura auren zaurawa sama da 1,000 a Kano
Wasu daga cikin jama'ar da ta halarci taron daurin auren a babban masallacin Juma'a na cinkin birnin Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: