Boko Haram: Yadda wata tsohuwa ta ceci ran wata jaririya ta hanyar ba ta nono a yayin gudun tsira da rai
-Wata tsohuwa maikmanin shekara 50 ta ceci ran wata jaririya jikarta ta hanyar ba ta fatar nononta ta na tsotasa a yayin gudun tsira da rai
-Tsohuwar mai suna Aisha Modu ta dauki 'yar ne bayanda mahaifiyarta ta rasu 'yan BBoko Haram kuma suka kashe babanta a wani hari da suka kawo kauyensu, wanda haka ya sa suka yi gudun tsira da rai
A wani labari mai sosa rai wata tsohuwa jihar Borno ta ceci jaririyar da 'yar ta haifa ta mutu, ta hanyar ba ta fatar nononta a yayin da suke tserewa daga hannun Boko Haram tsawon kwanaki suna tafiyar kafa ba kuma abinci.
Tsohuwa mai suna Aisha Modu mai kimanin shekara 50, wacce ta sha da kyar daga hannun Boko Haram, na dauke da jaririyar da 'yar ta ta haifa ne ta kuma mutu, a cewar jaridar Daily Mail.
Aisha ta bayar da labarin iftila'in ne a lokacin da suka isa wani dakin shan magani na kungiyar agaji na Save the Children a jihar Borno mai fama da rikicin Boko Haram.
'Yar tsohuwa Aisha na cewa, "Da tsakar dare muna cikin barci sai wata makwabciyata tashe ni a ta ce min na dauki abin da zan iya dauka mu gudu a lokacin da 'yan Boko aram su ka kai hari kauyenmu".
Aisha ta kuma ce, "'Su na ta harbin kan mai uwa da wabi, girman harsashinsu zai kai girman yatsa na, amma da haka muka fito, ni ya ke ni ba zan iya gudu ba, sai suka kama ni tare da wasu mazaje wadanda su suka kuma yiwa wani daga cikinsu yanka Rago a gabana".
Ba ci, ba sha, ga jaririya ga kuma wahalar tafiya haka 'yar tsohuwa Aisha ta ba rika ba jarririyar fatar nononta wanda ba ruwan nonon ciki sosai ta na tsotsa.
Kuma da haka da kuma taimakon Allah suka kai ga tudun mun tsira na wani dakina shan magani na kungiyar bayar da agaji ta Save the children.
A cewar Dakta Bot likitan da ya duba jaririyar da kakarta Aisha, "hakika ta shigo da jaririyar jikarta cike da damuwar halin koshin lafiyar jaririyar saboda halin da suka shiga kafin su iso nan".
"Da na tambayeta irin taimakon da ta samu kafin ta iso nan sai ta ta fashe da kuka, ta kuma bamu labarin dukkannin abin da ya faru a garesu kafin su iso nan, jaririyar da kakarta na cikin koshin lafiya a yayin da suke samun kulawar ma'aikatan lafiya".
Kungiyar agaji ta Save the Children ta ce, da akwai mata masu yawa a kauyukan jihar wadanda ke shayar da jariran wasu matan a sakamakon yawan mace-macen mata da ake samu a yayin haihuwa.
Kungiyar Boko Haram ta dade tana kai hare-haren ta'addanci a jihar Borno a inda ta yi sanadiyar rasa rayukan mutane da yawa tare da salwantar dukiya da kuma raba mutane da yawa daga muhallinsu
Yanzu dai hanklula sun soma kwantawa a wasu yankunan jihar bayan da rundunar Soji ta samu nasarar fatattakar 'yan ta'addan daga dajin Sambisa a karshen shekarar 2016.
Ga zanga-zangar goyon bayan Buhari
Asali: Legit.ng