Ga wata sabuwar kungiya a jihar Kaduna
- Gwamna Nasir El Rufai yayi gargadi akan wata sabuwar kungiya mai suna Gausiyya
- Yan jarida sun gudanar da wata bincike wanda ya bayyana cewa shugaban kungiyar na zaune a wata kauye wajan Zaria
- Sheikh Isma’il Bn Sayyadi Yusha’u yace kungiyar ba wata sabuwar kungiya bace, kawai su yan Tijjaniyya ne
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El Rufai, ya kawo kuka akan wata sabuwar kungiya a jiha Kaduna wacce zata iya zama hadari fiye da Boko Haram.
Bayan an gudanar da bincike cikin ayyukan da sukeyi, gwamnatin jihar Kaduna ta yanke shawaran cewa kada a bari su zauna a jihar Kaduna saboda abubuwan da sukeyi ya saba koyarwan addinin musulunci.
Jaridar Daily Trust ta gudanar da bincike wanda ya bayyana cewa shugaban kungiyar na zaune a wata kauye wajan Zaria da kewaye.
Yayinda yan jarida suka kai garin Makarfi, shugaban kungiyan baya nan domin Magana. Da muka koma lokacin a biyu, Malam Salisu Abubakar yak i yin wani Magana yana cewa wanda ya cancanta yayi Magana shine shugaban kungiyar.
Tare da shugabannin kungiyar na garin Makarfi, yan jaridan sun tafi Madinatu Zaria, inda shugaban kungiyar ke zaune.
Madinatu Zaria na nan ne a garin Zaria, Kofar Gayan da Amana Mai Kasuwa a karamar hukumar Igabi na jihar Kaduna.
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng