Wata mata ta kona mijin ta saboda yayi mata kishiya

Wata mata ta kona mijin ta saboda yayi mata kishiya

Wata labari mai kama da almara da ya faru a garin Jos dake arewacin Najeriya ya jefa kowa cikin rudani inda wata mata mai suna Hafsat ta kona mijin ta don ya yi mata kishiya.

Ita dai Hafsat da mijin ta suna zaune ne da mijin ta shekaru 8 kenan bayan sun shafe shekaru 6 suna soyayya kafin aure a wata unguwa dake a cikin garin Jos.

Wata mata ta kona mijin ta saboda yayi mata kishiya
Wata mata ta kona mijin ta saboda yayi mata kishiya

Al amurra dai sun fara tsami a tsakanin su tun bayan da mijin nata mai suna Mubarak ya yanke shawarar zai sake aure inda ita kuma ta nuna masa sam hakan ba zai yiwu ba.

To bayan dai an yi auren ne a watan Janairun da ya wuce kuma har ma amaryar ta tare a wani gidan ta dake a wata unguwa sai mai afkuwa ta afku.

Lamarin dai ya faru ne wata rana bayan da mijin ya dawo daga gidan amaryar sa sai matar tace kada ya kuskura ya shigo mata gida don kuwa idan ya shigo to ya kuka da kan sa. Ai kau mijin na shigowa sai ta watsa masa ruwan zafi inda kuma duk jikin sa ya toye.

Yanzu haka dai yana asibiti yana karbar magani.

Allah ya kyauta.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel