DA DUMI-DUMI: Sako daga Likitan Buhari

DA DUMI-DUMI: Sako daga Likitan Buhari

Farfesa Sadiq Suleiman Wali wanda ke zaman tsohon likitan shugaba Buhari a wancan lokacin da yiyi mulkin soja ya yi kira da yan Najeriya su kara hakuri da yanayin da shugaban ya shiga su kuma ci gaba da yi masa addu'a.

DA DUMI-DUMI: Sako daga Likitan Buhari
DA DUMI-DUMI: Sako daga Likitan Buhari

Farfesa Sadiq ya yi wannan kiran ne a cikin wata fira da yayi da jaridar Daily Trust wanda kuma a buga a yau asabar din nan 25 ga watan Fabrairu.

Da aka tambayeshi game da ra'ayin sa da kuma shawarar da zi iya ba yan Najeriya, sai yace "Ina ga abun da yafi kamata shine mu dukufa wajen yi masa addu'a don samun lafiyar sa don kuma dawo war sa gida lafiya."

KU KARANTA: Masana sun gano duniya 7 a sama

Haka zalika da aka tambayeshi shawarar da zai ba shi shugaba Buharin sai ya kada baki yace: "Shawarar da zan bashi shine ya daure yabi umurnin likitocin sa".

A wani labarin kuma dai Shugaba Muhammadu Buhari yayi Magana da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, a wayan tarho.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da tashan muryar Amurka.

Yace: "A ranan asabar nayi Magana da shugaba Buhari a waya kuma yana nan da lafiya. Duk masu yada jita-jita akan lafiyarsa su canza tunaninsu.

‘’Shugaban kasan nah utu ne domin duba kansa wanda ke nan cikin kundin tsarin mulkin Najeriya mataimakinsa yam aye gurbinsa har sai ya dawo."

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel