Wani mutumi yayi ma kazaman Almajirai wanka a Maiduguri (Kalli hotuna)
Ana kiran yaran dake yawo a wasu yankunan Najeriya, musamman yankin arewacin kasar da suna Almajiri.
An samo kalman Almajiri ne daga yaren Larabci wato Al-Mahaajirun, wato ma’ana malami mai sani wanda ke isar da sakon addinin Islama.
Lokuta da dama zaka ga cewa yaran Almajirai sun kasance maza daga tsakanin shekaru hudu da 15. Ya kamata ace suna koyan karatu a karkashin kulawar wasu malaman Qur’ani. A maimakon haka sai ka gansu a unguwanni inda suke bara don tafiyar da rayuwansu.
Al’umman gari na kula dasu ta fanni daban-daban. Wasu na daukan su sannan su basu kulawa ta musamman. Wasu kuma na basu sadaka da abinci a duk lokacin da suke da damar yin haka.
KU KARANTA KUMA: Hadaddun hotuna 10 na kyawawan ‘ya’yan masu kudin Arewa
Wani dan Najeriya ya yanke shawarar sauya salo ta hanyar yiwa wasu yaran Almajirai wanka. Ance ya tattara wasun su ya kuma yi masu wanka a kyauta.
Wani mutumi da aka kira da Abdullahi Yusuf ya yada hoton kasa tare da rubuta: “Naga wannan a wani gurin wanke mota a nan Maiduguri, kuma koda dai hakan zai zama wani iri ga wasu, amma ni na karfafa wa mutumin gwiwa da ya ci gaba. Ya tattara Almajirai wadanda ke cikin kazanta sannan yayi musu wanka a kyauta. Na bashi kudi ya siya sabulu saboda ya ci gaba da basu kulawar wanka a kyauta ga yaran da basu da wanda zai yi musu wanka da kyau wanda yana da matukar muhimmanci ga lafiyarsu.”
Ance wannan ya faru ne a ranar Alhamis da misalign karfe 1.15 na rana a wani gurin wanke mota deke kusa da massallacin Indimi a Damboa Road Maiduguri.
Mutane da dama sun yaba ma bawan Allan kan abunda yayi.
Yayi kyau!
Asali: Legit.ng