Ikon Allah: Masana sun gano wasu duniyoyi guda bakwai a sama
- Masana falaƙi sun ce sun gano wasu duniyoyi da ke kewaya wani tauraro mai nisa, wanda kuma ke da yanayin da za iya rayuwa a cikinsa
- Masanan, wadanda suka fito daga kasashe daban-daban, ciki har da Amurka da Burtaniya da Belgium, sun ce sun gano duniyoyin bakwai ne, wadanda kowace girmanta ya kai duniyar da muke ciki, suna kewaya wani tauraro mai suna Trappist-1
An yi amannar cewa nisan duniyoyin daga tauraron ya yi daidai da yadda za a iya samun ruwa a cikinsu.
Masana kimiyya na fatan samun damar yin cikakken nazari a kan duniyoyin nan gaba, ta hanyar amfani da na'urorin hangen nesa.
Amma za a iya daukar daruruwan shekaru kafin mutane daga wannan duniyar tamu su iya zuwa can.
KU KARANTA: Valencia ta suburbudi Real Madrid
A wani labarin kuma, Masana masu hange da binciken Duniya sun bayyana cewa za a samu husufin rana a sassan kasar nan a Ranar Lahadi. Ko da yake dai masanan sun ce abin ba wani mai kamarin gaske bane.
Kungiyar bincike game da cigaban sararai na kasa watau NASRDA tace wannan abu zai faru ne karshen makon nan kamar yadda ta fadawa hukumar dillacin labarai na kasa NAN jiya a Birnin Abuja.
Masanan sun ce wannan abu zai faru ne a ko ina na fadin kasar. Hasken ranar za ta fi raguwa ne kuma a Yankin kudancin kasar irin su Fatakwal, Kalaba da Garin Uyo. Inda kuma abin ba zai yi wani tasiri ba shi ne Yankin Arewacin kasar musamman Jihar Kebbi.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa
Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng