Ýan wasan Super Eagles guda 4 waɗanda basa wasa da Sallah
Wani abin mamaki dangane da Najeriya shine karfin imanin addinansu, saboda kana taba su zasu fada maka cewa ai su musulmai ne ko kirista ne, sai su nemi ma su nuna maka su aka saukar ma addinin ma gaba daya.
Don haka mun dauko muku cikakken jerin yan wasan Najeriya da basa wasa da Sallah sakamakon su musulmai ne.
1. Ahmed Musa
A shekarar 1992 ne aka haifi Ahmed Musa, 14 ga watan Oktoba, takamaime a garin Jos, babban birnin jihar Filato. Musa ya fara wasan kwallon kafa ne a kungiyar GBS dake Jos a shekarar 2008, daga nan ya koma kungiyar JUTH a shekarar 2009, sa’annan ya buga ma Kano Pillars, kafin ya wuce nahiyar Turai, inda yake wasa a kungiyar Leicester City.
Ko abokanan wasansa sun shede shi cewar baya wasa da Sallah.
KU KARANTA: Dansanda yayi ma tsohuwa fashi da makami
2. Shehu Abdullahi
A yanzu haka Shehu Abdullahi yana buga ma kungiyar Anorthosis Famagusta, inda yake buga musu bangaren tsakiya. Shehu Abdullahi ba zai taba mantawa da marigayi Stephen Keshi ba, saboda shine wanda ya janyo shi zuwa Super Eagles.
An haifi Shehu a garin Sakkwato, a can ya girma, shima kowa yayi masa shaidar baya wasa da ibada.
3. Rabiu Ibrahim
An haifi Rabiu a shekarar 1991, kuma a yanzu haka yana wasa akungiyar K.A.A.Gent, inda yake rike musu lamba 10. Shi kam Rabiu ya sha yin aikin Hajji da Umarah, ba sau daya ba sau biyu ba.
4. Ramon Azeez
Wani dan wasan Najeriya da shima baya wasa da Sallah shine Ramon Azeez, an haifi Ramon a 12 ga watan Disambar 1992, kuma yana taka tamola a kungiyar UD Almeria dake kasar Sifen.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng