Nesa ta zo kusa: An fara aikin gadar Neja-Delta

Nesa ta zo kusa: An fara aikin gadar Neja-Delta

– Da alamu nesa ta zo kusa don kuwa an kama hanyar wani babban aiki a Neja-Delta

– An soma aikin gadar nan ta 2nd Niger wanda tun tuni ake ta waka

– Wani babban Jami’i yace ‘yan kwangila sun dawo bakin aiki

Nesa ta zo kusa: An fara aikin gadar Neja-Delta
An kusa fara aikin gadar Neja-Delta

Ga mutanen Neja-Delta da alamu nesa ta zo kusa don kuwa ‘yan kwangila sun koma bakin aikin shahararriyar gadar nan watau ta 2nd Niger kamar yadda shugaban NSIA na kasa Mista Orji Uche ya bayyanwa manema labarai jiya.

Idan har an kammala wannan gada za ta hada Garin Asaba da Onitsha, watau dai za ta hada yankin kudu maso gabas da kudu maso kudu na Neje-Delta. Tun lokacin mulkin shugaba Jonathan dai ake ta wakar za a yi aikin amma har yanzu shiru.

KU KARANTA: Makarantun da Buhari yayi karatu

Mista Orji yace an sasanta da ‘yan kwangila wanda yanzu haka sun koma bakin aiki, abin da kawai ya rage shi ne harkar kudi wanda yanzu ake kokarin ganin yadda za su fito nan da ‘yan watanni masu zuwa. Za dai a kai akalla shekarar 2020 ana wannan namijin aiki.

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya saki kudin wasu manyan kwangiloli jiya daga ciki akwai kwangilar ginin titin kan iyaka tsakanin Najeriya da kasar Kamaru wanda zai ci har Dala Miliyan 38 da kuma wani babban titi a gabashin kaduna mai kilomita 15 wanda zai ci sama da Naira Biliyan 32.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel