Jaririn da aka haifa mai kai biyu ya riga mu gidan gaskiya
Wata mata mai shekaru 30 ta haifi wani jariri mai ban al’ajabi a kasar Indiya, shi dai wannan jaririn halittarsa tazo ne da kai guda biyu.
Sai dai kash! Jaririn ya rasu awanni kalilan bayan haihuwarsa.
Mahaifiyar jaririn ta haife shi ne ta hanyar tiyata, wanda aka yi a babban asibitin SP dake kasar Indiya, kuma ta bayyana ma likitoci bata da masaniyar yanayin halittar jaririn.
KU KARANTA: Shema ya musanta tuhumar sata akansa, kotu ta bada belinsa akan naira biliyan daya
Yayin da take yi ma yan jarida bayani, mahaifiyar tare da mahaifin yaron sun shaida ma manema labarai cewa sai a jajibarin tiyatan ne suka samu labarin yanayin halittar jaririn nasu, kamar yadda wata jarida ta ruwaito.
Iyayen yaron, Muhammad da Nasreen sun fahimci halittar yaron nasu ne bayan daukan hoto da aka yi ma cikin matar, sai dai iyayen sun ce ba zasu taba kyamar yaron nasu ba duk da irin halittar daya zo da shi.
Bayan haihuwar jaririn, sai likitoci suka bayyana yaron a matsayin dan baiwa, inda iyayen yaron suka ce wannan baiwa ne daga Allah. Likitoci sun bayyana cewar yiwuwar samun jariri mai kai biyu daya ne cikin haihuwa 100, 000.
Kamar yadda masana suka ce, ana samun jariri mai biyu ne idan kwan dake cikin mahaifar mace basu rabu da juna ba bayan saduwa da maniyyi.
“sai dai yawancin jarirai masu irin wannan halittan suna mutuwa ne saboda gabobinsu basa iya daukan dawainiyar su.” inji masana.
Kashi 40 na jariran da ake haifa a hade suna mutuwa ne kafin a haife su, yayin da kashi 35 kuwa suna mutuwa ne bayan haihuwarsu.
Ga wani bidiyon jarirai da aka haifa a hade:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng