Yanda na musulunta Inji wani tsohon tantirin Kirista

Yanda na musulunta Inji wani tsohon tantirin Kirista

Wani saurayi mai suna Ishaq Mustaqim ya bayyana yadda ya karbi addinin musulunci bayan da yana tantirin dan iskan Kirista.

Yanda na musulunta Inji wani tsohon tantirin Kirista
Yanda na musulunta Inji wani tsohon tantirin Kirista

Wani matashi mai suna Ishaq Mustaqim ya karbi addinin Musulunci ya kuma bada labarin yadda ya bar addinin Kirista da kuma lokacin da yake tsula tsiyar sa a gari.

Ishaq Mustaqim matashi ne wanda ya rasa kan gado ya shiga fitsaranci a gari tun yana yaro karami dan shekara 13. Ishaq na balaga ya cika 18 sai gidan yari aka wuce da shi na shekaru 3. Ishaq dai tun yana karamin sa tsohon tantirin dan iska ne.

KU KARANTA: Sun rotsawa dan sanda kai

Mustaqim wanda asalin sa Kirista ne, ya koma karanta littafi mai arziki na Bible har kuma yana zuwa ibada jifa-jifa idan ya ga dama. Bayan ya fito daga kurkuku ya shiga neman kudi ko ta halin kaka, dama can bai kammala karatu ba.

Ishaq Mustaqim ya shiga neman kudi ido rufe, ya kuma same su; ya saye motoci da gidaje ko da yake a otel yake kwana, nan fa aka kara samun sa ya shiga hannu, aka kara wucewa da mutumin gidan maza na kusan shekara. A kurkuku Ishaq ya hadu da wani Musulmi, in takaice maka labari, yanzu ya zama Musulmi ya tuba da duk wadancan abubuwa na baya.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga dai Bidiyon Ishaq yana bayani yadda ya tuba; Ishaq yace kudi ba su bane rayuwa:

Asali: Legit.ng

Online view pixel