Zaƙaƙurin ɗan Arewa Jelani Aliyu, maƙerin hamshaƙan motocin alfarma

Zaƙaƙurin ɗan Arewa Jelani Aliyu, maƙerin hamshaƙan motocin alfarma

Yan Najeriya da dama sun yi suna a duk fadin duniya ta bangarorin daban daban, cikinsu akwai wani dan tsatson yankin Arewa, kuma Bahaushe, Jelani Aliyu wanda shine ya kera motocin alfarma na Chevrolet Volt na kamfanin General Mootors dake Amurka.

Zaƙaƙurin ɗan Arewa Jelani Aliyu, maƙerin hamshaƙan motocin alfarma
Zaƙaƙurin ɗan Arewa Jelani Aliyu, maƙerin hamshaƙan motocin alfarma

Kimanin shekaru 24 da suka gabata ne Jelani Aliyu ya tashi daga Sakkwato birnin Shehu zuwa jihar Detroit dake kasar Amurka masu jajayen kunnuwa, a yanzu dai Jelani ne babban mai tsarawa tare da shirya yanayin cikin motocin kamfanin GMC, inda a shekarar 2007 ya tsara yadda motar nan ta alfarma Chevy Volt zata kasance, wanda masana suka bayyana motar a matsayin daya daga cikin manyan motocin alfarma a duniya gaba daya.

Tarihin Jelani

An haifi Jelani Aliyu ne a shekarar 1966, inda ya zamo na 5 a cikin yaran su 7 da iyayensa suka haifa, kuma tun yana karami Jelani ya samu ingantaccen Ilimi, na muhammadiyya dana boko, wanda yace hakan ya taimaka sa sosai.

Zaƙaƙurin ɗan Arewa Jelani Aliyu, maƙerin hamshaƙan motocin alfarma
Zaƙaƙurin ɗan Arewa Jelani Aliyu, maƙerin hamshaƙan motocin alfarma

Jelani yayi makaranatar firamari ta Sokoto Capital School daga shekarun 1971 zuwa 1978, daga nan sai ya wuce kwalejin gwamnatin tarayya dake Sokoto a shekarun 1978 zuwa 1983 don karatun sakandari, inda ya samu kyautan dalibi mafi kwarewa a fannin zanen kimiyya.

KU KARANTA: Yan Najeriya na cigaba da bayyana mabanbanta ra’ayoyin dangane da tafiyar shugaba Buhari

cikin wata hira da yayi, Jelani Aliyu yayi bayanin abinda ya bashi sha’awar shiga harkar kere keren motoci:

“dama ina da sha’awar zane zane, ina zana duk wani abin da na gani, mutane, dabba, bishiya da duk wani abin d azan iya yin tunani. Tun ina yaro ina son ilimin kimiyya, musamman a finafinai zaka ding ganin abubuwan ban mamaki.

“Sa’annan ina son motoci, duk dayake a lokacin babu motar Ferari a jihar Sakkwato, amam dai ina ganinsu a jaridu, kuma suma sun sa min sha’awar zane zane. Don haka sai na hada sha’awta na son zane zane, da son motoci, da haka na yanke shawarar kasancewa mai zana motoci.”

A shekarar 1986, Jelani ALiyu ya fara karatun gaba da sakandari a jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, sai dai bai dade ba, ya koma kwalejin kimiyya da fasaha na jihar Kebbi, inda ya karanci kimiyyar zane zane, kuma ya kammala a shekarar 1988, inda ya lashe kyautan dalibi mafi hazaka.

Zaƙaƙurin ɗan Arewa Jelani Aliyu, maƙerin hamshaƙan motocin alfarma
Zaƙaƙurin ɗan Arewa Jelani Aliyu, maƙerin hamshaƙan motocin alfarma

Bugu da kari Jelani Aliyu ya dangana duk cigaban daya samu a rayuwa ga iyayensa, tare da gode musu saboda goyon baya da suka bashi. Jelani yace:

“iyayena basu musanta abinda nake sha’awar karantawa ba, sun kyale ni in zani duk abinda nake son karantawa, kuma suka bani goyon baya. misali, lokacin da naje jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, amma sai na yanke shawarar fasawa, iyayen sun bani goyon baya, kuma suna da fahimta sosai.”

Fara aikin Jelani Aliyu a kamfanin General Motors

A shekarar 1990 ne Jelani Aliyu ya koma kasar Amurka, can jihar Detroit, inda ya jona karatu a kwalejin karatun kirkira a karkashin shirin daukan nauyin karatun dalibai na jihar Sakkwato, anan ne fa Jelani ya fara samun gogewa a harkar zane zane, Jelani ya nuna hazaka sosai a kwalejin, inda ya lashe kyaututtukan kamfanin motoci na Michelin, US, da Ford.

Zaƙaƙurin ɗan Arewa Jelani Aliyu, maƙerin hamshaƙan motocin alfarma
Zaƙaƙurin ɗan Arewa Jelani Aliyu, maƙerin hamshaƙan motocin alfarma

Sai a shekarar 1994 Jelani Aliyu ya samu takardar shaidar digiri a fannin zane zanen motoci, daga nan sai kamfanon General Motors ta dauki hazikin yaron aiki, da haka Jelani ya fara aiki a kamfanin. Wasu daga cikin manyan ayyuka da Jelani Aliyu yayi a kamfanin GMC sun hada da:

  1. Abokin aiki wajen kera motar alfarma ta Buick Rendezvous
  2. Jagoran tsara cikin motar Pontiac G6
  3. Hadin gwiwa da kamfanin Opel wajen kera motar ASTRA

Sai dai aikin da Jelani Aliyu yayi akan motar Chevrolet Volt ne ya fitar da sunansa a duk fadin duniya, kuma tauraron kamfanin GMC, a shekarar 2007 ne aka yi bajakolin motar a yankin Arewacin nahiyar Amurka.

Daga karshe zamu iya fahimtar kamfanin GMC sun yi sa’a babba da samun hazikin dan najeriya, musulmi, bahaushe kuma dan Arewa daya daga likafar kamfaninsu, kuma wannan hazikanci na Jelani ya kara ma yan Najeriya da dama kaimin shiga a fafata dasu a duk inda suka samu kansu a Duniya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng