Dangote ya gina sabon kamfanin sarrafa shinkafa a Arewa
Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote yace zai taimaka wa manoman shinkafa 15,000 a kasa Najeriya da kayayyakin noma da taki.
Dangote ya gina kamfanin sarrafa shinkafa a karamar hukumar Goronyo dake jihar Sokoto.
Ya kara da cewa kamfaninsa za ta fara da manoma 15,000 ne sannan a hankali ta na kara yawan manoman.
Yace zai kuma taimakawa manoman rake a jihar.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Sako daga fadar shugaban kasa
Bayan haka Dangote ya ce kamfaninsa za ta wadatar da kayan noma wa manoman kamarsu maganin feshi,ragar kare shinkafa daga tsuntsaye, irin shukawa da dai sauran su.
Ya kara yi wa manoman albishir cewa kamfanin na sa za ta koyar da manoman yankin yadda za su yi amfani da dabarun noma na zamani sannan kuma su kamfanin za ta siya shinkafar bayan sun noma.
Daga karshe ya ce wannan kawancen da za su hada da manoman zai taimaka wurin samar da aiki wa mutanen jihar daga mutane 15,000 zuwa mutane 50,000.
Asali: Legit.ng