Jarumar ‘Yar wasan kwaikwayo ta rabu da Mijin ta
– Jarumar ‘Yar wasan kwaikwayo Tonto Dikeh ta rabu da Mijin ta
– Ana zargin Mijin Tauraruwar ‘Yar wasar yana bin maza
– Tonto Dikeh ta Nollywood dai ta nemi a daina magana game da abin da ya wuce
Fitacciyar ‘Yar wasan kwaikwayon nan na Nollywood Tonto Dikeh ta rabu da Mijin ta kwanaki. Tonto Dikeh da Oladunmi Churchill sun yi aure kwanaki har suka samu d’a, sai dai yanzu da alamu auren ya zo karshe.
Wasu dai suna zargin tsohon Mijin ta yana bin maza, sai dai ba tace komai ba game da batun, asali ma dai ta nemi tsohon Mijin ta ya daina magana game da auren na su da yi ki armashi a bainar Jama’a. Ba dai yau aka fara samun irin wannan aure na Taurari ya samu matsala ba.
KU KARANTA: Ya yi wa uwar sa ciki kuma zai aure ta
Tonto Dikeh dai suna da yaro guda daya wanda ya kusa cika shekara guda a Duniya. A baya dai Tauraruwar tace Mahaifin yaron ya kan samu dama ya ga yaron, sai dai tsohon Mijin na ta yace karya take yi ba a basa damar ganawa da ‘dan na sa.
A can wani Gari a Kasar Zambia kuwa, wani matashi Farai Mbereko mai shekara 23 zai auri uwar sa mai shekaru 40. Kai kafin nan ma dai wannan yaro yayi wa Mahaifiyar ta sa ciki, yanzu tana da juna biyu na wata 6.
Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng