Musulunci: Shin wanene Annabi Muhammadu SAW?
Wadanda ba Musulmi ba sai ka ji su na tambaya wai kai kai shin ma wanene Annabi Muhammadu SAW? Musulman Duniya dai kaf sun yarda da Annabi Muhammadu SAW a matsayin farin Jakadan Allah Manzon sa, kuma na karshe cikin jerin Annabawa wanda kuma aka saukarwa Al-Kur’ani.
Kafin Manzon Allah SAW an yi Annabawa da Manzanni da dama, sai dai Annabi Muhammadu SAW shi ne cikamakin dukkanin Su. Annabi Muhammadu SAW ya kuma sha ban-ban da sauran saboda an aiko sa ne da Al-Kur’ani ga dukkanin Duniya baki daya.
An haifi Annabi Muhammadu SAW a Garin Makkah a Watan Afrilun shekara ta 571 Miladiyya, wanda ya zo daidai da Watan Rabi’ul Auwal. Iyayen Manzon Allah SAW sun rasu tun yana karami, asali ma Mahaifin sa Abdullahi dan Gidan Abdul-Mutallib bai ga haihuwar sa ba. Annabi ya tashi ne a gidan Baffan sa da kuma Kawun sa Abu-Dalib.
KU KARANTA: Kungiyar Izala ta na goyon bayan Sanata Shehu Sani
Manzon Allah SAW ya tashi Maraya ya kuma auri Nana-Khadija AS wanda ta girme sa a shekaru da dukiya. Ko da Manzo SAW bai taba rubutu ko karatu ba, an fara yi masa wahayi da babban littafi Al-Kur’ani lokacin da ya cika shekaru 40 a Duniya, hakan ta sa wasu suka shiga muzguna masa ko da sun san bai taba karya ba, wannan ta sa Manzo har ya bar Mahaifar sa ta Makkah.
A sannu a hankali bayan shekaru da dama Ubangiji ya daukaki Manzo SAW, ya shiga kusan ko ina a kasar larabawa, kafin ya bar Duniya dai sai da aka yi masa alkawarin cewa Addinin Islama zai ratsa fadin Duniya, hakan kuwa aka yi.
A cigaba da biyo mu…
A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook
https://www.facebook.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng