Ka ji abin da Gwamnati ta ce ayi a Yankin Neje-Delta

Ka ji abin da Gwamnati ta ce ayi a Yankin Neje-Delta

– Gwamnatin tarayya ta ba ‘yan kwangila umarni su koma Yankin Neja-Delta

– ‘Yan kwangila su cigaba da aiki a Yankin ko kuma a dauki mataki

– Za a hukunta wadanda suka yi taurin kai Inji Farfesa Osinbajo

Ka ji abin da Gwamnati ta ce ayi a Yankin Neje-Delta
Ka ji abin da Gwamnati ta ce ayi a Yankin Neje-Delta

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ba ‘yan kwangila umarni do su yi maza-maza su koma Yankin Neja-Delta domin cigaba da ayyukan da aka sa su. Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana haka kwanan nan.

Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana haka a wani taro da aka yi da masu ruwa-da-tsaki a Yankin a Jihar Imo kwanan nan. Shugaban kasan na rikon-kwarya yace abin na kuma ci masa tuwo a kwarya watau ganin yadda aka ki cigaba da kwangila da dama a Yankin.

KU KARANTA: Osinbajo na kokari - BBOG

Mai girma Osinbajo yace Kamfanin NNPC da Hukumar NDDC mai kula da Yankin Neja-Delta sun yi watsi da kwangilolin da suke yi don haka ya bada umarni a koma bakin aiki da gaggawa. Osinbajo ya sha alwashin cewa duk dan kwangilan da ya murkushe kudi ba tare da aiki ba zai ji a jika.

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo yana ta zagaye a Jihohin kudu da na Neja-Delta domin ganin an kawo karshe rikicin da ke Yankin. Haka kuma mun samu labari dai Kasar Amurka na shirin kashe makudan kudi domin ganin Najeriya ta samu wutar lantarki tsayayye.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng