Sarkin masarautar Borgu, mai murabus ya rasu

Sarkin masarautar Borgu, mai murabus ya rasu

Sarkin Borgu na jihar Neja mai murabus, Alhaji Isiyaku Jikantoro ya rasu jiya a wani asibiti mai zaman kansa, Bay Specialist Hospital a garin Minna.

Sarkin masarautar Borgu, mai murabus ya rasu

Sarkin mai murabus ya rasu yana da shekaru 67, ya rasu bayan ya sha fama da ciwon siga, kuma ya mutu ya bar mata daya da yaya bakwai.

KU KARANTA: Gurgun da sojoji suka casa ya samu gwaggwaɓan kyauta daga gwamnan Ebonyi

A shekarar 2000 ne dai Isiyaku Jikantoro ya zama Sarki, amma sai marigayi Halliru Dantoro yaki amincewa da nadin sabon Sarkin, inda ya mika lamarin ga kotu.

Anyi ta shari’a har zuwa kotun koli, inda kotun ta yanke hukuncin tsige Sarki Isiyaku jikantoro daga kujerar sarautar masarautar Borgu, daga nan sai yayi gudun hijira zuwa karamar hukumar Rijau na jihar Neja, inda marigayi sarkin Borgu Halliru Dantoro ya gaje shi a shekarar 2004.

Addu'ar mu a Legit.ng shine, Allah ya jikanshi da gafara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng