Yadda Boko Haram suka yima mijina da 'ya'yana hudu' yankan rago - inji wata bazawara

Yadda Boko Haram suka yima mijina da 'ya'yana hudu' yankan rago - inji wata bazawara

- Wata mata wadda 'yan kungiyar Boko Haram suka yanka mijinta da 'ya'aynta guda hudu ta labarta wa majiyar mu yadda al'amarin ya wakana

- Matar ta ce 'yan kungiyar sun je suka buga mata kofar daki har ma suka karya ta

Yadda Boko Haram suka yima mijina da 'ya'yana hudu' yankan rago - inji wata zawara
Yadda Boko Haram suka yima mijina da 'ya'yana hudu' yankan rago - inji wata zawara

Ta ce sun shiga kai tsaye zuwa dakinta, bayan da suka karya kofar dakin sannan suka fito da ita waje.

'Yan kungiyar sun dai je gidan matar ne da nufin kashe mijinta, a inda suka yi ta harbinta domin fada musu wurin da mai gidan nata yake.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun nunawa duniya makamman da suka kera

A wani labarin kuma, Gwamnatin Najeriya ta bawa rundunar ‘yan sandan kasar, daukar sabbin jami’ai dubu goma a duk shekara, domin kawo karshen rashin yawan jami’an tsaron da kasar ke fuskanta.

Babban Sifeton ‘yan sandan kasar Ibrahim Idris ya tabbatar da samun cigaban, yayinda yake jagorantar wani taro da manyan jami’an ‘yan sanda a birnin Abuja.

Sifeto Janar Idris, ya ce Karin ya zama tilas domin samun nasarar murkushe aikata miyagun laifuka a kasar.

Ya ce kara yawan jami’an ‘yan sandan zai canza alkalumman da ke aiki a Najeriya, da ya nuna cewa dan sanda guda ne ke lura da mutane 400 a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng