Dan majalisan Najeriya Sani Bello ya mutu
Sani Bello, wani dan majalisar wakilai dake wakiltan masabar tarayya na Mashi/Dvisi a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress, ya mutu.
Bello ya rasu ne a safiyar ranar Laraba, 15 ga watan Fabrairu. Yana da shekaru 51 a duniya.
Jaridar Premium Times ta ce Abubakar Adamu, wani mataimakin marigayi dan majalisar, ya bayyana cewa ya dauki tsawon watanni da dama yana fama da wani rashin lafiya da ba’a bayyana ba kafin rasuwar sa.
Adamu yace rashin lafiyan Bello yayi tsanani ne wasu yan makonni da suka wuce kuma an kais hi asibitin gwamnati a Kaduna amma abun bakin ciki ya rasu a safiyar ranar Laraba.
KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaban kasa Buhari na iya kiran Najeriya
“Ya rasu a safiyar yau 11:00 ta wuce da yan mintoci kuma a yanzu zamu tafi da gawarsa Katsina,” cewar Adamu.
Kakakin majalisa, Yakubu Dogara ya tabbatar da rasuwan dan majalisar a wata sanarwa inda yayi makokin marigayi dan siyasan.
“Marigayi abokin aikinmu ya kasance, mai tsari da yake raha da dukkan mambobin majalisan.
"Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan sa, gwamnati da kuma mutanen jihar Katsina da kuma abokan aikinsa da gwamnati da kuma mutanen Najeriya.
“Muna addu’a ga Allah da ya basu juriyan rashin da sukayi,” kakakin yace haka a sanarwa daga mataimakinsa na musamman a shafin zumunta da kula da al’amuran jama’a Turaki Hassan.
Marigayi Sani ya kasance dan majalisa na biyu da ya rasu a kan mulki cikin shekara.
Mutuwarsa yazo watanni bayan wani dan majalisa, Adewale Oluwatayo, dake wakiltan Ifako-Ijaiye a jihar Lagas ya mutu a Abuja.
Asali: Legit.ng