‘Rundunar sojan kasa zata ɗebi sabbin sojoji 12,000 a bana’ – Buratai

‘Rundunar sojan kasa zata ɗebi sabbin sojoji 12,000 a bana’ – Buratai

Babban hafsan sojan kasa, Laftanar janar Tukur Yusuf Buratai yace rundunar sojan kasa zata dauki sabbin kuratan sojoji 12,000 cikin wannan shekarar don bunkasa lamarin tsaro a kasar.

‘Rundunar sojan kasa zata ɗebi sabbin sojoji 12,000 a bana’ – Buratai
‘Rundunar sojan kasa zata ɗebi sabbin sojoji 12,000 a bana’ – Buratai

Buratai ya bayyana haka ne yayin dayake kare kasafin kudin rundunar na bana a gaban kwamitin dake kula da rundunar sojan kasa na majalisar wakilan kasar nan, inda yace da zarar sun amince da kasafin kudin rundunar daya kai naira biliyan 152.8, za’a fara shirin daukan sabbin sojojin.

KU KARANTA: ‘Muslunci ne maganin dukkanin matsaloli’ inji masu karajin aiki da shari’ar musulunci a kasar Ingila (bidiyo)

Buratai yace za’a ayi daukan sabbin sojojin ne kashi biyu, inda kashin farko rundunar zata dauki sojoji dubu shidda (6000), daga bisani kuma su kuma daukan wasu dubu shidda.

Buratai ya cigaba da fadin cewar a yanzu haka Sojoji na gudanar da aiki a jihohi 32 a fadin kasar nan inda suke yaki da miyagun mutane daban daban da suka hada da masu garkuwa da mutane, yan ta’adda, masu fasa bututun mai, masu satar shanu da sauransu.

Babban hafsan bai tsaya nan ba, ya koka kan yadda ba’a sakar ma rundunar isassaun kudade, wanda yace hakan na kawo tsaiko ga gudanar da ayyukansu, inda ya roki da yan majalisun su taimaka wajen magance ma rundunar wannan matsalar da take fuskanta.

Wasu daga cikin yayan kwamitin da suka hada da Rima Shawulu sun koka da halin da sojoji ke ciki, inda suka bukaci Buratai daya tabbatar da matsuguni masu kyau ga sojoji.

Daga karshe, kwamitin ta yanke shawarar gayyatar kwamitin kula da rundunar sojin kasa na majalisar dattawa don su hada kai wajen yanke shawara dangane da wasu batutuwa da suka shafi rundunar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel