Wakokin da suka fi kowane wannan shekarar

Wakokin da suka fi kowane wannan shekarar

– An raba kyaututtukan waka na ‘grammy’ ga zakarun da suka yi fice bana

– Mawakiya Adele ta ci taro a Ranar

– Tauraruwa Beyonce tayi wasa a wurin

Wakokin da suka fi kowane wannan shekarar
Wakokin da suka fi kowane wannan shekarar

Kwanan ne aka raba kyauttukan waka na shekarar bara na lambar grammy. Mawakiya Adele ce dai ta lashe kyaututtuka da dama a wurin taron.

Haka kuma shahararriyar Mawakiyar nan watau Beyonce tayi wasa a wurin da cikin tagwayen ta. Adele ta buge Beyonce wajen lashe kyaututtukan shekarar inda kundin wakar ta ta fi ta kowa. Haka kuma Mawaki Chance the Rapper ya lashe lambobi da dama ciki akwai kyautar sabon shigan da ya fi kowa a shekarar bara.

KU KARANTA: Ka san Diyar Buhari Hannan mai hoto?

Sauran Mawaka irin su Lil-Wayne da Drake sun samu wasu kyaututtuka da ba za a rasa ba daga wakokin na su. Manyan mawaka da makada na Duniya dai sun halarci wannan gagarumin taro wanda an dade ana yin sa a ko wace shekara.

A kwallon kafa kuma Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo wanda shi ne zakaran duniya na bana ya nemi wata budurwa mai suna Lilia Ermak amma abu ya faskara. Lilia Ermak dai tana zama ne a Birnin Miami kuma tayi fice a Duniya wajen harkar gayu, da alamu dai ba ta son Tauraron Dan wasan na Real Madrid.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel