ALBISHIR: Hukumar kula da gidan yari zata dauki ma'aikata 6,545

ALBISHIR: Hukumar kula da gidan yari zata dauki ma'aikata 6,545

- Shugaban hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya watau Nigerian Prisons Service (NPS) Ja’faru Ahmed a jiya ya bayar da haske game da shirin da hukumar sa take yi wajen samun izinin daukar ma'aikata har 6,545 a matsayi daban-daban

- Shugaban Ja’faru Ahmed ya kuma ce shirin zai lakume zunzurutun kudi har N6biliyan don cimma nasarar hakan

ALBISHIR: Hukumar kula da gidan yari zata dauki ma'aikata 6,545
ALBISHIR: Hukumar kula da gidan yari zata dauki ma'aikata 6,545

Kontolan ya kuma sanar da cewa hukumar tasa tana nan zata fito da wani shiri don bunkasa harkar noma irin na zamani a gidajen yarin fadin kasar nan domin yan gidan yarin su rika ci da kan su da kansu.

Kontrola Ahmed Jafar ya yi wannan bayanan ne lokacin da yake kare kasafin kudin hukumar sa a gaban wani kwamiti mai kula da harkokin kasafin kudin inda ya kara jadda yadda hukumar tasa take fama da karancin ma'aikata.

KU KARANTA: An sake yin APC sak a jihar Yobe

A wani labarin kuma, Wasu masana tattalin arziki a Najeriya sun ce kimanin kashi 20 cikin 100 na tsabar kudin da ake kashewa a kasar na jabu ne.

Daya daga cikinsu, Dr Obadia Mailafiya, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, ya shaida wa BBC cewa hakan na barazana ga tattalin arzikin kasar, wanda tuni ya fada mawuyacin hali.

A cewarsa ma'aikatan babban bankin kasar na hada baki da bankunan kasuwanci domin sake dawo da kudaden da suka tsufa cikin sha'anin hada-hadar kudi.

Dr Mailafiya ya ce, "idan kudade suka tsufa akan tara su ne a kone, sannan a kera wadanda za su maye gurbinsu.''

Asali: Legit.ng

Online view pixel