Wai wanene Murtala Muhammad

Wai wanene Murtala Muhammad

– A rana irin ta yau aka kashe Janar Murtala a shekarar 1976

– Su Laftana Kanar Dimka suka kashe Murtala a cikin mota a Legas

– Janar Obasanjo ya karbi mulki a bayan rasuwar shugaban kasar

Wai wanene Murtala Muhammad
Wai wanene Murtala Muhammad

Janar Murtala ya karbi mulkin kasar nan ba tare da an kashe ko dan tsako ba a Ranar 29 ga Watan Yulin 1975. A wancan lokaci shugaban kasa Yakubu Gowon ba ya kasar. A lokacin yakin basasa Murtala yayi namijin kokari lokacin yana rike da babban bataliya ta biyu.

A dan lokacin da Murtala yayi mulki don kuwa bai wuce kwanaki 200 ba rak. Ya sallami ma’aikata da dama domin gyara harkar kasar har da tarin Sojoji. Murtala ya fara shirin mikawa farar hula mulki bayan wani lokaci da kuma maida Birnin Tarayya zuwa Garin Abuja tare da yi wa tsarin kasar garambawul. Ko da ya rasu kafin nan, hakan kuwa aka yi.

KU KARANTA: Rashin Buhari na kawowa Najeriya cikas

Bayan an kashe Janar Murtala dai, Janar Obasanjo ne ya karbi mulkin. Janar Obasanjo ya harbe wadanda suka kashe Janar Murtala Muhammad har lahira. A wancan lokaci Muhammadu Buhari ya rike Gwamnan tsohuwar Jihar Borno.

A yayin da matar Janar din ta ke jiran sakon farin ciki watau ana shirin bikin ranar Valentine na masoya, sai kwatsam kawai ta ji labarin mutuwar Mijin na ta. An dai birne Janar Muratala a Garin Kano. Masana sun ce da ace yayi tsawon rai da Najeriya ta ga sauyin gaske.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng