Uwar bari?: ‘A shirye nake nayi sulhu da Kwankwaso’ – Ganduje
Bayan kwashe sama da shekara guda ana takun saka tsakanin gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje da tsohon gwamnan jihar sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a yanzu gwamna Ganduje yace kowa ya mayar da wukarsa cikin kube, a dawo teburin sulhu a shirya.
Dangantaka tayi tsami tsakanin jiga jigan yan siyasan biyu ne tun bayan ziyarar ta’aziyya da Kwankwaso ya kai ma gwamna Ganduje bayan rasuwar mahaifiyarsa, inda magoya baya suka shirya ma Kwankwaso gangami.
KU KARANTA: Sanata Orji yace kasada ne sanata ya dinga fada da gwamnan jihar sa
Gwamna Ganduje yace akwai bukatar a samu sulhu tsakaninsa da tsohon maigidan nasa kuma tsohon abokin siyasa, Ganduje ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da manema labarai a satin daya gabata, inda yace “menene matsalar idan aminai, kuma abokan siyasa suka sulhunta tsakaninsu?
“Sanin kowa ne ba’a taba samun abokan siyasa kamar mu ba a duk fadin kasar nan.” Inji shi
Ganduje ya kara da fadin yana goyon bayan duk wani shirin sulhu tsakaninsa da Kwankwaso dari bisa dari
Gwamnan yayi wannan hira da manema labarai ne bayan ya kaddamar da azuzuwa guda 2000 wadanda gwamnatinsa ta gina su a cikin kwaryar Kano a shekaru biyu da suka kwashe suna mulki, gwamnan yace a shirye yake ya magance duk wata matsala da ta addabi ilimi a matakin farko a jihar.
Gwamna Ganduje yace gwamnatinsa ta samar da wata asusun hadin gwiwa tsakaninta da kungiyoyi masu zaman kansu da al’ummai daban daban tare da sauran masu ruwa da tsaki don ganin an warware duk wata matsala data dabaibaye harkar ilimi a jihar Kano.
Daga karshe gwamnan ya bayyana ma yan jaridu cewar tuni gwamnatinsa ta fitar da naira biliyan 1, wanda ta baiwa gwamnatin tarayya a matsayin nata gudunmuwar, inda ita kuma gwamnatin tarayyar ta bayar da naira biliyan 1 ita ma don tallafa ma cigaban ilimi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng