Yau shekaru 41 kenan da kisan Janar Murtala Muhammad

Yau shekaru 41 kenan da kisan Janar Murtala Muhammad

A rana irin ta yau a shekarar 1976 ranan 13 ga watan Febrairu ne aka kashe tsohon shugaban kasan soja, Janar Murtala Mohammed a wata yunkuri na juyin mulki da aka yi masa a ranan Juma’a 13 ga watan Febrairu.

Yau shekaru 41 kenan da kisan Janar Murtala Muhammad
Yau shekaru 41 kenan da kisan Janar Murtala Muhammad

An kashe Janar Murtala ne tare da mai gadinsa wata ADC yayinda suka tsaya a cikin mota. Yan Najeriya na tunawa da wannan babban rashi saboda abubuwan cigaba da manufofi masu kyau da Janar Murtala ya kawo ma kasa.

KU KARANTA: Donald Trump zai yi waya da shugaba Buhari a yau

Sashin Hausa na jaridar mmuryar Amurka tayi hira da wani kwamishinan ‘yansanda Alhaji Hammawa Njidda Damare wanda ya shaida kisan Janar Murtala Mohammed.

Daya daga cikin abubuwan da yayi shine canza babban birnin tarayya daga jihar Legas zuwa Abuja, kirkiro sabbin jihohi guda 7.

Matasan jiya irinsu Yusuf Etham da Jonah Morris Mangapila da sukayi karatu a waje ba zasu taba mantawa da Janar Murtala Mohammed ba saboda irin alherin da yayi musu.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Asali: Legit.ng

Online view pixel