An kai mace mafi nauyi a duniya asibiti domin jinya a Indiya
Wata mata yar shekara 36 yar kasan Misra mai suna Eman Ahmed, wacce ake sa ran itace mace mafi nauyi a duniya mai nauyi kilo 500 an kaita birnin Mumbai domin aikin Tiyata.
Ta shiga Mumbai ne ckin wata jirgin shata wanda ana sa ran idan aka gudanar da Tiyata kanta, zata rage nauyi.
Ta kasance tana famam da ciwon bugun jinni wanda ya sabbaba kafanta sa hannunta ya salance kuma ya shafi magananta, saboda ceton rayuwan Eman, ana neman mata taimako a yanar gizo.
Ana jinyata a asibitin Saifee a Mumbai,, inda akayi mata dakin jinya na musamman mai babban kofa da gado. Ma’aikacin asibitin yace.
Za’a gudanar da Tiyata akanta amma kafin nan za’ayi gwaje-gwaje domin rage mata kiba.
https://twitter.com/naijcomhausa
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
Asali: Legit.ng