Mummunan hatsarin mota tayi sanadiyar mutuwar mutane 22 a hanyar Kano-Kaduna
- Malam Sa’idu-Daura yace wasu mutane 58 kuma sun ji rauni daban daban
- Sa’idu-Daura ya kuma bayyana cewa, wandada sun ji rauni suna Asibiti a Tashar-Yari
- Ya fada cewa, baban motan ya dibi kayayyaki da yawa; mutane da kuma itace
Game da wajen mutane 22 suka rasa rayuwarsu a wani hatsari da ya faru a hanyar Kano zuwa Kaduna.
KU KARANTA: Dalibar jami’a ta hallaka sanadiyar sakacin likita
Mummunan hatsari ya faru a yau, Juma'a, 10 ga watan Faburairu a lokacin da taya wani mota mai lamba WDL 502 XA ta fashe akan titi.
Kwamandan masu tsira da hanyoyi wato Federal Road Safety Commission (FRSC) ta garin Tashar-Yari, Ahmed Sa’idu-Daura, da yake wajen da hatsarin ya faru a daidai Tashar-Musa, karamar hukumar Makarfi, ya tabbatar da maganan.
KU KARANTA: Wani Gwamna ya kai ziyara asibiti, abun da ya gani zai baka takaici
Mal. Sa’idu-Daura ya kuma bayyana cewa, wanda sun ji raoni na frimare healthcare centre a Tashar-Yari.
Ya ce: ''Masu jin rauni a hatsarin mota suna da yawa, zaa kai su asibitin Jami'ar Ahmadu Bello dake garin Zaria daga karamin asibitin.”
KU KARANTA:
Ya kuma ba masu tukin mota shawara akan kar suna gudu da kuma kwashe yawan kaya da mutane.
Ya ce: “Ina son fada ma masu tukin mota cewar, su kula rayuwar mutanen da suke cikin motan suna hannu su ne.”
Asali: Legit.ng