An kama matar aure tana cikin aikata masha’a tare da aminin mijinta (HOTUNA)
- An kama wata matar aure mai yara biyu tana lalata da aminin mijinta
- Agnes Ukwim Phiri ta kasance tafi jin dadin aminin mijinta fiye da shi mijin nata
- Su dukka mazan guda biyu yan sanda ne a ofishi daya. Koda dai matar ta gudu ba’a ganta ba, amma babu wanda yasan abunda zai faru idan mazajen biyu suka hadu.
An kama wata mata tana lalata tare da mijin wata da rana tsaka.
Masu wucewa kan hanya sun kama wata Agnes Ukwim Phiri, matar aure mai yara biyu, a cikin wani mota inda suke jima’i tare da aminin mijinta.
KU KARANTA KUMA: Wata mata ta cizge kan azzakarin saurayinta yayin wani musu bayan coci
A take mutumin ya gudu inda ya bar abokiyar masha’ar sa tare da masu wucewa inda suke ta daukar hotunan matar.
An rahoto cewa matar tayar da motar mutumin zuwa inda ba’a sani ba.
Tuni dai hotunan matar ya yadu a yanar gizo, tare da mata da dama dake ihu suna kiran matar da sunaye daban daban. An rahoto cewa mazajen guda biyu jami’an yan sanda ne a Chipata.
Kalli bidiyon wani miji maci amana da aka kama:
Asali: Legit.ng