Manyan matsaloli da ke kawo tasgaro ga cigaban Arewa
Yankin Arewa shine yanki masi girma a cikin yankunan kasar najeriya guda uku, da suka hada da yankin kudanci, inda yan kabilar Inyamurai suka fi yawa, sai kuma yankin yammacin kasar nan inda yan kabilar yarbawa suka fi shahara, da kuma yankin Arewan kanta, inda Hausawa suka fi yawa, amma akwai wasu kabilu da dama duk a yankin.
Sanin kowa ne a baya da can, tun bayan samun yancin mulkin kasar nan, Arewa abin tinkaho ce ga kasar gabaki daya, ta yadda idan tayi atishawa, sai duk sauran yankunan sun kamu da rawar sanyi, wannan karamci da daukaka da Arewa ta samo ya biyo bayan irin jajircewa da iya mulki na su Gamji dan Kwarai, wato Ahmadu Bello Sardauna suka yi, tare da ire irensu su Alhaji Abubakar Tafawa Balewa, Sir Kashim, Aguyi Ironsi, Maitama Sule da dai sauran sa’anninsu na dauri.
Amma abin takaici sai ga shi a yau Arewa ta zama abin yi ma dariya, ana yi mata cin kashi, ta ko ta ina Arewa bata da katabus. Da wannan ne zamu yi duba ga wasu daga cikin abubuwan da suke kawo ma Arewa tasgaro ga cigabanta.
KU KARANTA: 'Zamu mayar da Sojoji gida ga iyalansu" - Buratai
Wasu daga cikin matsalolin da Arewa ke fuskanta sun hada da:
1-Jahilci
2-Matsalar tsaro
3-Rashin aikinyi ga matasa
Jahilci: a da ilimi muhimmin lamari ne ga al’ummar Arewa, don kuwa duk inda ake zuwa ayi karatu a samu difloma, digiri kai har ma da digirgir a duk duniyar nan, ba inda dan Arewa baya shiga a dama da shi.
Zamu iya gane haka idan mukayi duba da ire iren makarantun da Sardauna ya kafa a yankin, ciki har da jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, kwalejin kimiyya da fasaha dake Kaduna da sauransu, wadanda har yanzu babu kamarsu a duk yankin Arewa duk da cewa sun shafe sama da shekaru arba’in da assasawa.
Amma sai ga shi a yau an wayi gari yan Arewa ne masu kin karatu, dan arewa ne ya gwammace ya tafi jihar Legas ci rani ba yana aikin kaskanci, bayan ga makaranta nan a karamar hukumar su amma ba za shi ba saboda baya son karatun. Dan Arewa a yanzu ya fi son ya tura yaronsa yaje yawon bara da sunan talauci, ba tare da ya kais hi makaranta ba. A yau dan Arewa ya gwammace ya aurar da yarsa karama da sunan addini ba tare da ya bata koda ilimin firamari ba.
Toh Malam, ta yaya za’a samu cigaba a al’umma da jahilci, bayan wadanda ya kamata su kawo ma al’ummar cigaba sun tafi yawon ci rani, yawon bara da aurar da yara kanana ba tare da basu ilimi ba?
Matsalar Tsaro: sakamakon lalacewar sha’anin ilimi da nuna halin ko in kula ga ilimin kansa, sai aka dinga samun jahilai a kujerun shugabanci dana malanta, kaga kuwa babu yadda za’a samu zaman lafiya a irin wannan yanayi.
Haka ne ya haifar da jahilan mutane da suka fara yi ma addinansu daban daban fahimtar da ra’ayinsu yafi gamsu da shi. Wannan na daya daga cikin abin da ya haifar da irin su Boko Haram, Mai tat sine, Ombatse da sauransu.
Sai ga shi a yau mun wayi gari wani sabon matsala, rikicin makiyaya da manoma, wanda a yanzu idan ka cire Boko Haram babu abinda ke yi ma Arewa barazana kamar rikicin Manoma da makiyaya. Shima rikicin kabilanci tsakanin manyan kabilu da kanana ba’a bar sa a baya ba.
Idan ka hada alkalumma da rikice rikicen nan, zaka samu cewa ba dubun dubatan rayuka ne aka yi asarar su, wadanda dukkaninsu al’ummar Arewa ne. ta yaya za’a samu cigaba a haka?
Rashin aikin yi: ko dai da gangan, ko kuma sakaci da rashin iya gudanar da shugabanci na gari, shine dalilin daya sanya matsalar rashin aikin yi kamari a cikin al’ummar mu.
Sai dai, a nan ma ba zaka raba wannan matsalar da jahilci ba, amma yayin da wanda bai yi makaranta ba ya rasa aikin yi, toh fa tabbas maganan zaman lafiya bai ma taso ba. Saboda zai ba kansa aikin yi ne ta hanyar sace sace da dauke dauke, ko kuma shaye shaye.
A tsakanin jihar Kano, Borno, Sokoto, Katsina da Kaduna, daruruwan kamfununuwa ne suka durkushe, don haka dole suka sallami ma’aikatansu, wani hali kake tunanin ma’aikatan nan da iyalansu zasu shiga?
Kana ganin ba sai yadda hali yayi ba, ko kuma idan mutum mai tsoron Allah ne? to ta kaka za’a cigaba a haka?
Ya kamata dai shuwagabannin siyasa dana gargajiyar yankin Arewa su kara dagewa kamar yadda suke yi a yanzu wajen ganin sun hada kawunan al’ummominsu don a samu zaman lafiya mai daurewa, da haka ne kawai za’a fara gina sabon ginshikin samun cigaba a al’ummar Arewa.
Da fatan zamu ji, kuma mu fadaka.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga yadda Alha Maitama Sule ya wasa Sir Ahmadu Bello Sardauna:
Asali: Legit.ng