Kaciyar mata ta kazanta a kudancin Najeriya (Karanta)

Kaciyar mata ta kazanta a kudancin Najeriya (Karanta)

- Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ta bayyana matukar fargaba kan yawaitar yi wa mata kaciya a jihohin Osun da Ebonyi da ke kudancin Najeriya

- A wata sanarwa da ofishin UNICEF a Najeriya ya fitar albarkacin ranar yaki da yi wa mata kaciya ta duniya, babban jami'in hukumar, Mohammed Fall, ya ce ana yi wa mata fiye da kashi 77 cikin 100 kaciya a jihar Osun

Kaciyar mata ta kazanta a kudancin Najeriya (Karanta)
Kaciyar mata ta kazanta a kudancin Najeriya (Karanta)

Ya kuma ce jihar Ebonyi ce ta biyu wajen kaciyar ta mata, a inda ake yi wa kashi 74 cikin 100 na matan jihar kaciyar.

Bisa ga wani bincike na harkar lafiya da aka yi a 2013 a kasar, jihohin Ekiti da Imo da Oyo ne ke biye wa Osun da Ebonyi baya wajen yi wa mata kaciyar.

Mista Fall ya ce, bincike ya nuna cewa kaciyar mata ba ta da wani amfani a tsarin lafiya, illa ma dai ta kara wa wadanda aka yi wa kuncin rayuwa.

Da man dai babban jami'i Hukumar ta UNICEF, a jihohin Imo da Ebonyi, Mista Benjamin Mbakwem, ya ce ana yi wa kashi 68 cikin 100 na matan jihar kaciya.

Ya bayyana haka ne a wurin wani taro na bayar da horo ga ma'aikatan lafiya a matakin-farko.

A cewarsa, bincike ya nuna cewa mata bakwai cikin 10 na rayuwar kunci saboda ana yi musu kaciya.

Mista Mbakwem ya ce: "Su kansu mutanen da ake yi wa kallon masu ilimi ne suna yin wannan dabi'a."

Hukumar Lafiya ta Duniya dai wato WHO, ta sanya ranar 6 ga watan Fabrairun kowace shekara ta zama ranar Yaki da yi wa mata kaciya a Duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng