An yiwa shugabannin kananan hukumomin Borno kakkabar yayan kadanya
- Gwamnan jihar Barno Kashim Shetima ya amince da rusa shugabannin kwamitocin riko na kananan hukumomin jihar
- Kwamishinan kananan hukumomin jihar Zanna Usman ne ya sanar da hakan a garin Maiduguri
Zanna ya ce gwamnan ya amince da hakanne bayan shugabannin sun cika adadin zamansu a kujerun shugabancin kananan hukumomin.
Ya Kara da cewa dukkansu sun kammala adadin watanni shida da dokar kananan hukumomin jihar ta bayar.
Gwamnatin ta umarci kowannensu ya mika ragamar mulkin karamar hukumarsa a hannun sakataren karamar hukumar kafin gwamnati ta nada sababbi.
A wani labarin kuma, Shugaba Muhammadu Buhari ya aikewa da Majalisar Kasa bukatar kara kwanakinsa a birnin London domin karbar sakamakon gwaje - gwajen lafiya da likitocinsa suka yi masa.
Shugaba Buhari ya shirya dawowa Abuja a yammacin yau, amma likitocinsa suka shawarci ya kammala karbar sakamakon kafin ya dawo Nijeriya.
Daga birnin na London, Shugaba Buhari ya bayyana godiyarsa ga 'yan Nigeria sakamakon kulawa, addu'o'i da fatan alherin da suke yi masa.
Asali: Legit.ng