Jihar Sokoto ta fara aiwatar da sabon tsarin albashi ga malaman makarantun gaba da sakandare

Jihar Sokoto ta fara aiwatar da sabon tsarin albashi ga malaman makarantun gaba da sakandare

- Malaman makarantun gaba da sakandare za su dara da sabon tsarin albashin CONTISS da gwamnatin jihar ta shirya soma biya

- An dade ana kai ruwa rana da gwamantocin baya kan amafani da tsarin albashin amma hakan bata yiwuwa sai wanna lokacin

Jihar Sokoto ta fara aiwatar da sabon tsarin albashi ga malaman makarantun gaba da sakandare
Jihar Sokoto ta fara aiwatar da sabon tsarin albashi ga malaman makarantun gaba da sakandare

Malaman makarantun gaba da sakandare a jihar Sokoto sun yabawa gwamna Aminu Waziri Tambuwal bisa cika alkawarin sa na aiwatar da sabon tsarin albashi wanda aka fara a watan da ya gabata.

Tuni dai malaman kwalejin kimiyya da fasaha ta Umaru Ali Shinkafi da kwalejin koyon aikin koyarwa ta Shehu Shagari dukansu mallakin gwamnatin jihar su ka ce su na wata addu'a ta musamman don godewa Allah da ya nuna masu karshen fadi tashin da su ke don ganin an aiwatar da tsarin albashin.

Fafutukar ganin an aiwatar da tsarin ta fara ne a shekarar 2008 biyo bayan kaddamar da tsarin albashin malaman makarantun gaba da sakandare (CONTISS), kuma duk da cewa sun yi ta kokarin ganin gwamnatocin baya sun aiwatar da tsarin, a wannan shekarar kadai ne su ka ci nasara.

Da ya ke magana game da batun, shugaban kungiyar malaman kwalejojin ilimi reshen kwalejin Shehu Shagari, Abubakar Arzika cewa ya yi gwamna ya gama nasa kuma dukkan malamai za su sauke nasu nauyin.

Ya ce sun dade su na shirya addu'o'i na musamman na neman dafawar Ubangiji, "yanzu ga shi burinmu ya cika, za mu shirya wata addu'ar ta musamman don godiya ga Allah a kuma yi wa gwamnati addu'a bisa aniyar ta ta kyautatawa jama'a."

A nasa bangaren, shugaban reshen jihar Sokoto na hadaddiyar majalisar ma'aikatan gwamnati ta kasa, Abubakar S. Malami, cewa ya yi tabbatarwa cewa shi gwamna ne mai son ma'aikata, Tambuwal ya cancanci yabon duk wani ma'aikaci.

"Muna da kwarin gwiwa cewa a hankali dai duk bukatunmu za su biya."

Da ya ke fadin hikimar aiwatar da sabon tsarin albashin, mai magana da yawun Tambuwal, Malam Imam Imam, ya ce an kawo tsarin ne don samun ingancin aiki kuma don daga darajar makarantun gaba da sakandare na jihar Sokoto.

Babban dalilin kaddamar da dokar ta baci a bangaren ilimi a jihar Sokoto shi ne don kawo gyara a dukkan matakai — firamare da sakandare da kuma na gaba da sakandare.

Ba wai kawai gwamnati ta rika sabbin gine-gine da gyara tsaffi ba, muna cika alkawarin mu ga malamai da sauran ma'aikata.

Na tuna lokacin wani taro da lakcarori game da zabubbukan 2015, gwamnan ya yi alkawarin aiwatar da sabon tsarin albashin, kuma ga shi yau alkawarin ya cika.

Gwamnati ba za ta gajiya ba a kokarin ta, kuma muna bukatar lakcarori da su ramawa kura aniyar ta ta hanyar kwazo don cigaban ilimi a jihar Sokoto."

Baya ga ma'aikatan kwalejin kimiyya da fasaha da na kwalejin ilimi, su ma na kwalejin sharia da darussan addinin musulunci watau Legal da na kwalejin aikin gona sun amfana.

Haka kuma, ma'aikatan kwalejin koyon aikin jiyya da ungozoma da na kwalejin aikin lafiya, Gwadabawa an biya su ne da sabon tsarin albashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: