LABARI DA DUMI-DUMI: Shugaba Buhari ba zai dawo gobe ba saboda wadannan dalilai
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari a sati biyu da suka wuce ya gaya ma yan Najeriya cewa zai tafi garin Landan a kasar Ingila da kuma zai koma a Litinin, 6 ga watan Faburairu
- Amma, akwai alamomi cewa shugaban ba zai koma a ranan gobe ba domin jami'i mai hudda da jama'a na fadar shugaban kasa mai suna Femi Adesina ya rubuta kan shafin Facebook sa yayin da yana bayyana cewa an dakarta da hutun Ogansa saboda umarnin likitoci
Yan Najeriya suke ci gaba da yi addua a madadin Shugaba Buhari domin a sati da ya wuce akwai jita-jita cewa shugaban Najeriya ya mutu.
KU KARANTA KUMA: Abinda Buhari keyi kowani ranan Allah - Femi Adesina
Amma fadar shugaban kasar da ministoci sun musanta wanna rade-raden.
Ga hoton da bayanai
Ku karanta sakon a kasa:
SHUGABA BUHARI YA DAKATAR DA HUTUNSA, YA RUBUTA ZUWA GA MAJALISAR DOKOKIN KASA
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika wata takarda ga majalisar dokokin kasa a yau, Lahadi, 5 ga watan Faburairu, inda yake bayyana niyyarsa ya dakarta da hutunsa domin yana so kammala jinya da kuma karbe sakamakon iri-irin gwaji da yayi kan shawarar likitocinsa
Shugaban yana so koma Abuja a daren yau, amma an bayar shawara da ya gama gwajinsa. An tura sakon zuwa ga shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai Honarabul Yakub Dogara.
Shugaban kasa yana bayyana godiyansa ga yan Najeriya kan damuwansu da addu’ansu kuma
Sanarwa daga FEMI ADESINA
Mai Magana da yawun shugaban kasa
Lahadi, 5 ga watan Faburairun 2017
Asali: Legit.ng