Dalillin da yasa aure ke saurin mutuwa a arewacin Najeriya – Farfesa Asabe Usman

Dalillin da yasa aure ke saurin mutuwa a arewacin Najeriya – Farfesa Asabe Usman

Farfesa Asabe Usman na jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto tayi bayanin dalilan da yasa aure ke saurin mutuwa a arewacin Najeriya.

Dalillin da yasa aure ke saurin mutuwa a arewacin Najeriya – Farfesa Asabe Usman
Dalillin da yasa aure ke saurin mutuwa a arewacin Najeriya – Farfesa Asabe Usman

Farfesa Asabe Usman yayinda take Magana a lakcan farfesosi na jami’ar tace aka kebe mata a kusan komai a arewacin Najeriya.

Tace kasancewan mace a arewa wani abin bakin ciki ne saboda ba’a daukan komai na ‘ya mace da muhimmanci.

KU KARANTA: Ibori ya gudu bai tsira ba

“Ana kuka a ko ina; ko ina a duniya ‘ya mace na kuka. Kukan zan iya bambanta amma ko ina ana yi.

“Wadannan koke-koken na nuna yadda mata ko shan wahala wajen fada a aji a cikin jama’a saboda akwai mazajen da ke ganin ba kamata tayi Magana ba.

“Maganan shine za’a iya jin muryan mace ta hanyar rubuce-rubuce da fahimtar mu na mata ta yanda zamu iya bayyana abubuwan aka dade bamu iya bayyanawa."

Yayinda take bayani akan kebecansu da akeyi da kuma zalunci saboda al’umma da ake ciki, Farfesa Asabe Usman ta nuna bacin ranta akan cewa ba dauki mace komai ba tamkar batada amfani.

Daga cikin bakin cikin kasancewa mace musamman a arewacin Najeriya. Farfesa Asabe Usman tace tilasta mata auren ba tare da son suba babban abun damuwa ne.

Game da cewarta, aure a arewacin Najeriya na mutuwa cikin sauki saboda yawancin iyaye na bayar da yayansu mata ne kawai ba tare da ra’ayinta ba.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: