Gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin aurar da zaurawa 1500

Gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin aurar da zaurawa 1500

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da shirye-shiryen ta na daukar nauyin aurar da zaurawa 1,500 a jihar.

Gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin aurar da zaurawa 1500
Gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin aurar da zaurawa 1500

Shirye-shiryen wanda gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya tabbatar zai ja gwamnatin jihar ta kashe miliyoyin naira a kan bikin zaurawan.

Mista Ganduje ya bayyana hakan ne a yayin rarraba kayan tallafi na sama da naira miliyan 130 ga mata da matasa 1560 a gidan gwamnatin jihar Kano.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa Saraki da Dogara suka kuma haduwa da Osinbajo

Gwamna Ganduje yace an bayar da tallafin ne domin matasa da mata su dogara da kawunansu a karkashin wannan koma bayan tattalin arziki da kasar ke ciki.

Yace har ila yau gwamnatin ta samar da kayayyakin gona sama da 520 ta kuma rarraba su ga manoma, tare da naira dubu biyar (N5000) ga dukkan wadanda suka amfana domin fara ban ruwa.

Gwamnan ya gargadi wadanda suka amfana daga tallafin kayayyakin wanda suka hada da injin din yin gugguru, keken dinky da kuma kayayyakin aski da kada su siyar da kayayyakin.

Yace nan bada jimawa ba za’a gama gurin koyar da sana’a a fanonni sama da 24 a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel