Matar wani mazaunin Lagas ta mutu a lokacin jima’i tare da saurayi

Matar wani mazaunin Lagas ta mutu a lokacin jima’i tare da saurayi

Matar wani mazaunin jihar Lagas ta mutu a gidan saukan baki bayan jima’i da saurayinta.

Matar wani mazaunin Lagas ta mutu a lokacin jima’i tare da saurayi
Matar wani mazaunin Lagas ta mutu a lokacin jima’i tare da saurayi

A cewar jaridar The Punch, matar da aka bayyana sunanta a matsayin Josephine, ta mutu a ranar Talata, 31 ga watan Janairu, bayan taje gidan saukan baki tare da saurayinta, Augustine Dunkwu, a yankin Isheri Olofin na jihar Lagas, da misalign karfe 2.30 na rana.

An tattaro cewa, Josphine ta suma bayan jima’i na kimanin mintoci 45 kuma anyi zargin cewa saurayin nata ya gudu bayan ya kasa farfado da ita.

Bayan saurayin nata ya fito shi kadai, sai mai kula da baki na gidan saukar bakin ta fara zargin wani abu tunda ya fito shi kadai, sai taje dakin don duba abunda ake ciki kuma anan ne taga cewa matar bata cikin hayyacin ta.

Daga nan ne ta sanar da ma’aikatan gurin sannan kuma aka bi sahun wanda ake zargin, aka kama shi sannan kuma aka mika sa hannun yan sanda a yankin Idimu.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun kwato makamai, motoci bayan arangama da yan Boko Haram

Wata majiya ta tabbatar da cewa Josephine matar wani mazaunin Lagas ne, wanda yaki yarda a bayyana sunan sa. Yace: “Tare suka sha lemo a gidan saukan baki kafin su tafi daki inda suka yi jima’i. Akwai yiwuwar cewa mutumin yayi amfani da mgani ko kuma matar bata da karfin da zata jure ma jima’in. Ta mutu a cikin halin.”

A yanzu an mika al’amarin ga hukumar binciken laifuka na jihar, a Yaba.

Jami’ar hulda da jama’a na jihar Lagas, Dolapo Badmos, ta bayyana cewa ana nan ana gudanar da bincike. Tace: “An bayyana mana cewa a ranar 24 ga watan Janairu, wanda ake zargi da marigayiyar sun yada zango a wani gidan saukar baki.

“Daga baya wanda ake zargin ya fito ba tare da bakuwarsa ba, wanda daka bisani mai kula da gidan tabi sahun sa.”

“An komar dashi dakin nasa inda gawar buduwar tasa yake ba tare da alamun rikici ba.

“An dauki gawar sannan aka kai dakin ajiye gawa na babban asibitin cikin gari dake, Yaba. Ana gudanar da bincike.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng