Kun ji abunda za'ayiwa karuwan Abuja?
- Yadda matsalar Karuwanci ke kara muni a Abuja babban birnin Najeriya al’amarin da ya sa Gwamnati ta sake kaddamar da kwamiti don kawar da wannan annoba.
- An dai kaddamar da kwamitin ne don shawo kan matsalar karuwancin da yanzu haka ta zama ruwan dare a kusan dukkan lunguna da sakuna na fadin birnin tarrayyar.
Kwamitin dai ya kunshin manyan mutane da kuma masu ruwa da tsaki a harkar tsaro dama sauran sannan gwamnati da dama.
A wani labarin kuma, Gwamnatin hadin gwiwar Austria ta amince ta hana mata saka burka a wurin taruwar jama'a kamar makarantu da kotuna.
Kasar tana kuma duba yiwuwar hana ma'aikatan kasar saka dankwali da wasu tufafi masu alaƙa da addini.
Ana ganin wannan shawara a matsayin wani yunƙurin daƙile 'yancin da jam'iyyar masu ra'ayin rikau, wanda dan takararsu ya sha kaye da kyar a zaben shugaban kasar na watan da ya gabata ke ci gaba da samu.
A makon da ya gabata ne gamayyar jam'iyyu masu matsakaicin ra'ayi suka kusa rugujewa sakamakon wani rikici a kan wata yarjejeniya game da makomar gwamnatin.
Asali: Legit.ng