Abun al'ajabi: Ku kalli hotunan yarinyar da bishiya ke tsiro a jikinta

Abun al'ajabi: Ku kalli hotunan yarinyar da bishiya ke tsiro a jikinta

-Wani abu kamar bawon bishiya na fitowa a fuskar wata yarinya 'yan shakara 10 da ya haifar da damuwa ga iyayenta

-Likitoci sun yi ittifakin cewa ita ce mace ta farko a tarihi da ta taba kamuwa da irin wannan matsala da a baya ake ganin ya fi addabar maza

-A baya dai a kasar an samu da wadanda suka kamu da irin wanna larurar an kuma yi musu aikin tiyata.

Yarinyar da bishiya ke tsiro a jikinta
Yarinyar da bishiya ke tsiro a jikinta tare da mahaifinta a gadon asibiti

Wata yarinta mai suna Sahana Khatun 'yar shekara 10 ta gamu da wata matsalar lafiya da ta daure wa likitocin Bangladesh kai.

Matsalar cutar da yarinyar game da ita ce na wani tsiro mai kama da ɓawon bishiya ya fara bayyana a fuskarta tun kimanin wata huɗu da ya wuce, mahaifinta bai damu ba.

Labarin yarinyar wanda sashin Hausa na BBC suka sa a shafinsu na intanet a ranar Laraba 1 ga watan Fabarairu BBC, ya ce mai haifinta bai ankara ba har sai ciwon ya soma fara yaɗo, sannan ya damu matuƙa, tare da garzayawa Dhaka babban birnin Bangladesh don neman magani daga kauyensu.

Yanzu likitoci na fargabar cewa Sahana ka iya zama mace ta farko da ta taɓa fuskantar abin da ake kira "larurar tsirowar bishiya a jiki".

Idan gwajin da suka yi ya tabbata, yarinyar ta shiga rukunin wasu mutane 'yan ƙalilan a faɗin duniya da ke fama da wannan larura mai suna epidermodysplasia verruciformis.

A shekarar da ta wuce wani mai suna Abul Bajandar ya yi fama da irin wannan matsala, amma yanzu ya warke.

Hannuwan Abul Bajandar duk wani tsiro ya fito musu inda suka yi girman kilogram biyar, ga kuma wani tofo a ƙafafuwansa, idan ka gan shi tamkar bishiya.

Mutumin mai shekara 27, shi ne ɗan ƙasar Bangaladesh na farko da aka gano na ɗauke da cutar kuma a yanzu an yi masa aiki har sau 16 a asibitin kwalejin koyon aikin likitanci ta Dhaka.

Mahaifin Sahana, Mohammad Shahjahan ya ce "Mu talakawa ne. 'Yata ta rasa mahaifiyarta tun tana 'yar shekara shida. Ina da kyakkyawan fatan cewa likitoci za su sassaƙe ɓawon bishiyar da ke fitowa a kyakkyawar fuskar 'yata."

Likitoci na fatan cewa larurar Sahana ba irin azababbiyar nan ba ce, don haka tana iya samun sauƙi cikin hanzari.

Ku cigaba da bin mu a Facebook a http://www.facebook.com/naijcom ko kuma a Tuwita a http://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel