Amfanin Aya ga lafiyar jiki

Amfanin Aya ga lafiyar jiki

Idan har yanzu ka na kokwanton amfani da aya, to ya zama lallai ka karanta wannan makalar don samun bayanai game da aya, amfaninta da illolinta.

Amfanin Aya ga lafiyar jiki
Amfanin Aya ga lafiyar jiki

Aya wata 'yar itace ce da ke girma a bangaren arewacin duniya inda ake samun yanayi mabambanta. Amma a zamanin yau ta samu shuhura a Turai.

Aya tana da dandano mai gardi kuma ta yi kama da kwakwa amma ta dan fi kwakwa zaki.

Alfanun noman aya shi ne, in dai ana kula da ita, tana bayar da amfani mai kyau, bayan haka kuma tana karawa kasar da aka shuka ta albarka.

Tana dauke da sinadaran magnesium da calcium da kuma iron. Tana samarwa da jiki sinadarin protein da kuma lafiyayen kitse. Tana kunshe da sinadarin vitamin B wanda ya ke amfanar da fata da gashi da kuma farata.

Don samarwa da jiki sinadaran vitamin da minerals, ya na da kyau a rika cin gram 70 zuwa 50 na aya a kullum.

Aya tana da amfani saboda tana kara karfin garkuwar jiki. Ta yawan amfani da ita, za ka gano cewa kusan ba ka rashin lafiya kuma za ka ji dadi sosai. Wannan aba tana inganta yanayin da mutum ke ciki, tana tsawaita kuruciya, tana karfafa yanayin gudanar jini sannan tana kara kuzari na zahiri da na boye.

Haka kuma tana da amfani ga sha'anin da ya shafi ciki da hanji, tana dauke da sinadarin da ke hana cushewar ciki da kuma kumburi.

Har ila yau tana taimakawa wajen rage sinadarin kwalestaral mara kyau a cikin jini. Za ka tserar da lafiyar ka da kuruciyar ka da kyawu matsawar ana cin aya kullum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

iiq_pixel