Me yayi zafi: Soja ya kusa kashe wata Budurwa da duka
– Wani Soja ya kusa kashe wata Budurwa mai suna Jewel da duka
– Wannan abu ne ya faru da Budurwar tana kan hanyar zuwa Garin Onisha
– Yanzu haka wannan Budurwa tana Asibiti
Wani Soja mai suna Sulaiman Olamilekan ya kusa kashe wata Budurwa mai suna Jewel Infinity da duka a yayin da Budurwar ta ke kan hanyar ta na zuwa Garin Onisha. Wannan Budurwa dai ta kawo kukan ta ne ta shafin Facebook.
Wannan Soja dai ya kama Jewel da duka ne a madakatar Sojoji yayin da ta baro Garin Fatakwal zuwa Onisha. Wannan Budurwa tace yanzu haka tana cikin wani hali bayan mugun duka da ta sha hannun Soja.
KU KARANTA: Tofa: Dalibar Jami'a ta mutu yayin da ta kai ziyara waken Alaji
Abin da dai ya faru shine wannan matashin Soja ya tare su a motar su, inda ya nemi wannan Yarinya ta fito waje bayan ya zarge ta gulman sa. Ko da dai ta fito ya nemi ta tsuguna kasa ta ba sa hakuri, ita kuma tace faufau ba za tayi hakan ba, don kuwa ba ta masa laifi ba. Daga nan ne Sulaiman ya samo wani katan itace ya shiga yi mata duka har ta kai ya nemo wani katon karfe.
Tuni dai wannan Budurwa ta koma Barikin Soji da ke Fatakwal inda ta kai karar wannan Soja SULAIMAN OLAMILEKAN, da alamu dai dama yayi kaurin suna duk da bai dade da shiga cikin Sojin ba.
Kai Malam! Ka ga wani karfe da aka ce ya shiga buga mata a jiki.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook
https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ya kamata Buratai ya binciki wannan labari ko kuwa?
Asali: Legit.ng