Ina nan da rai na ban mutu ba – Inji Jamila Nagudu

Ina nan da rai na ban mutu ba – Inji Jamila Nagudu

- Jaruma ‘yar wasan finafinan Hausa Jamila Umar Nagudu ta karyata rade-radin da ake ta yadawa wai Allah yayi mata rasuwa.

- Jamila ta ce tana nan cikin koshin lafiya bata mutu ba kuma.

Ina nan da rai na ban mutu ba – Inji Jamila Nagudu
Ina nan da rai na ban mutu ba – Inji Jamila Nagudu

Ta fadi hakanne a wata sako na bidiyo da ta saka a shafinta na Instagram jiya Asabar.

A bidiyon Jamila ta ce a wannan lokacima za ta yi tafiya ne zuwa garin Kaduna daga Kano.

Tare da yan uwanta tana wasa da raha a tsakaninsu.

A wani labarin kuma, Zaharaddeen Sani babban jarumi ne a farfajiyar fina-finan Hausa domin kuwa a cikin shekaru 3 ya zama wani sananne wajen ma’abota finafinan a yankin Arewa.

An fi sanin sa da fitowa a Fina-finan a matsayin mugu ko kuma a mare mutunci inda yake nuna karewa da kuma jarumtarsa a hakan.

Gidan jaridar Premium Times ta yi hira da jarumin a Abuja inda ya fede mata biri har wutsiya akan yadda ya zama shahararren dan wasan fina-finan hausa, dangartakarsa da abokan aikinsa da kuma bangaren rayuwar soyayarsa.

Zaharaddeen Sani yace tun yana yaro yake kaunar kallon fina-finan kuma tun da ga lokacin yake sha’awar zama dan wasan fim.

Yace haduwarsa da Ali Nuhu ke da wuya sai mafarkinsa ta zamo gaskiya inda ya fara saka shi a fim dinsa na farko.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel