Wata sabuwa! Tsire da balangu na sa cutar 'Kansa' - Bincike

Wata sabuwa! Tsire da balangu na sa cutar 'Kansa' - Bincike

Wata Farfesa akan ilimin abinci musamman abinda ya shafi nama da ganyayyaki ta gargadi mutane da su daina cin gasasshen nama wato suya ko tsire ba tare da an yi musu hadi da kayan miya ba musamman Albasa da kabeji.

Wata sabuwa! Tsire da balangu na sa cutar 'Kansa' - Bincike
Wata sabuwa! Tsire da balangu na sa cutar 'Kansa' - Bincike

Masaniyar kuma Farfesa akan ilimin lafiyar jama’a da na abinci a jami’ar Najeriya dake Nsuka jihar Enugu Ngozi Nnam ta ce cin gasasshen nama haka kawai ba tare da irin wadannan hadin ba ya na kawo cutar daji wato (cancer).

Malamar tace saboda hayaki da wutar da ake yin amfani dashi wajen gasa naman yakan haddasa wata dafi da ke iya kawo cutar muddun ba an hada naman da albasa bane ko wadansu ganyayyaki kamar su kabeji da sauransu wanda hakan yak e kashe karfin wannan dafi ya lalatashi sannan ya zamo abin amfani ga jiki.

Bayan haka kuma ta yi kira da akula da kifi shima domin gasa shi ya na kawo irin wannna dafi da kan iya sa akamu da cutar daji din.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng