Kungiyar malamai makaranta za ta fara sabon yajin aiki
Kungiyar malamai makarantun Polytechnics (ASUP) ta fara gargadin yajin aiki na rana 5.
Yau ranar Litinin, 30 ga watan Disamba ne kungiyar malamai makarantun Polytechnics (ASUP) ta fara gargadin yajin aiki na rana 5 bayan wa'adin da ta yi wa gwamnatin tarayya ta kawo karshe.
Jaridar The Nation ra rahoto cewa kungiyar malamai makarantun Polytechnics ta kasa (ASUP) za ta fara gargadin yajin aiki na mako daya a yau, 30 ga watan Janairu.
KU KARANTA KUMA: ‘Yan bindiga sun hallaka mutane 5 a inda suka bude wa wata masallaci wuta
Malamai sun dauki wannan mataki ne domin nuna rashin amincewarsu da gwamnatin kasar a kan yarjejeniyar ta da ƙungiyar da kuma talafawa makarantun Polytechnic.
Shugaban hukumar Comrade Usman Dutse ya ce wa’adin da ƙungiyar ta ba gwamnatin tarayya ta shige a watan Disamba 2006 da ta gabata ba tare da wata kwakwaran bayyani daga gwamnati.
KU KARANTA KUMA: Rundunar sojojin kasar Najeriya ta mamaye ko’ina a Gambia
Ya ce wannan matakin gwamnati ya bar su ba tare da wata zabi ba ila su soma gargadi yajin aiki na kwana 5.
Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa
http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng