Rundunar sojojin kasar Najeriya ta mamaye ko’ina a Gambia
Rundunar sojojin kasar Najeriya ta mamaye ko’ina a kasar Gambia a matsayin wata dalilin tsaro ga sabuwar gwamnatin shugaba Adama Barrow.
Koda shike sabon shugaban kasar Gambia shugaba Adama Barrow ya karbi mulki a hannu yahya Jammeh, amma har ila yau jami’an sojojin Najeriya ke gudanar da tsaro a kasar.
Jaridar Daily Sun ta rahoto cewa ma’ajiyar makamai ta rundunar kasar Gambia ne rundunar sojojin Najeriya ta mamaye domin wasu dalilai ta tsaro.
KU KARANTA KUMA: An kai gwamnatin tarayya da rundunar sojin sama kara bisa jefa bom a sansanin 'yan gudun hijira
A cewar rahoton, wannan mataki na da alaka da da'awar cewa tsohon shugaban kasa Yahya Jammeh yana da wasu ma'ajiyar makamai a boye.
Rahoton ta kuma cewa hedkwatar rundunar sojin kasa ta tura ahakalla sojoji 1,500 zuwa kasar Gambia a matsayin wata ɓangare na shiga tsakani a kasashen yammacin Afirka (ECOMIG).
Jaridar ta ce, sojojin kasa kawai a ke bukata a matsayin kula da halin da ake ciki a kasar.
KU KARANTA KUMA: Jami'an shige da ficen Amurka sun fara hana musulmi shiga kasar
Duk da haka, har in halin da a ke ciki ya bukaci sojojin sama, hukuma za ta tura su da gagawa.
Amma rundunar sojojin sama ta Najeriya da kuma sojojin ruwa tuni sun koma gida bayan kammalar da manufofin tura su a kasar.
Darektan ba da labari kan tsaro Birgediya-Janar Abubakar Rabe ya tabbatar da dawowar sojojin kasa da kuma na sama a Najeriya.
Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa
http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng