Kwana sun kare: Mai mata 97 ya kwanta dama

Kwana sun kare: Mai mata 97 ya kwanta dama

– Bello Abubakar Masaba mutumin da ya auri mata barkatai ya riga mu gidan gaskiya

– Bello Masaba ya mutu yana da mata kusan 100

– Masaba yayi wasiyya da a rika aure

Kwana sun kare: Mai mata 97 ya kwanta dama
Kwana sun kare: Mai mata 97 ya kwanta dama

Idan ba a manta ba akwai wani ta’aliki mai suna Bello Abubakar Masaba, a Garin Bida ta Jihar Neja mai mata barkatai. Wannan mutumi dai yanzu Allah yayi masa cikawa a jiya Asabar bayan yayi ‘yar gajerar rashin lafiya.

Masaba dai ya yanke jinki ya fadi har sau biyu, daga karshen yace ga garin ku. Wata Jarida mai suna The Eagle ta bada labarin rasuwar wannan mutumi. Alhaji Mutairu Salahuddeen; wani mai magana a madadin wannna mutumi ya tabbatar da haka.

KU KARANTA: Sarki Muhammadu Sanusi II yayi gargadi

Bello Masaba dai kowa ya san sa da yawan mata, ace mai mata 97, yayi mata kusan guda 107, ya kuma rasu ya bar fiye da 80, bayan ya rabu da wasu da dama. Ya haifi ‘ya ‘ya sama da 185, sai dai wasu sun rasu, yanzu ya bar akalla guda 133.

Bello Masaba dai ya rasu ne jiya da rana, an kuma shirya jana’izar sa a Ranar yau da safe. Marigayin yayi wasiyya da a daina zinace-zinace a koma auren mata na addini. Masaba ya mutu yana da shekaru 93.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel