Fitacciyar marubuciya Buchi Emecheta ta mutu a Landan

Fitacciyar marubuciya Buchi Emecheta ta mutu a Landan

Fitacciyar marubuciyar nan 'yar Najeriya Buchi Emecheta ta mutu.

Fitacciyar marubuciya Buchi Emecheta ta mutu a Landan
Fitacciyar marubuciya Buchi Emecheta ta mutu a Landan

Bisa ga rahotanni ta rasu ne a gidanta da ke birnin London a jiya, 25 ga watan Janairu tana da shekara 72.

An haife ta a birnin Lagos ranar 21 ga watan Yulin shekarar 1944, cikin iyalan Alice Okwuekwuhe Emecheta da Jeremy Nwabudinke, dukkannin iyayenta sun fito daga Ibusa, jihar Delta.

KU KARANTA KUMA: LABARI DA DUMI-DUMI: Tsohon kyaftin din Kano Pillars ya mutu

Buchi Emecheta ta rubuta littafai fiye da ashirin a kan fannoni daban-daban, koda yake ta fi mayar da hankali kan 'yancin mata da irin fafutikar da suke yi.

Wasu daga cikin littafanta su ne: The Joys of Motherhood (1979), Second-Class Citizen (1974), The Bride Price (1976) da kuma The Slave Girl (1977).

Buchi Emecheta ta samu lambobin yabo da dama game da rawar da ta taka wajen bunkasa rubutun kagaggun labarai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel