Na kama matata tare da fasto dinta a kan gado – tsoho mai shekaru 60 ya fada ma kotu

Na kama matata tare da fasto dinta a kan gado – tsoho mai shekaru 60 ya fada ma kotu

Ya kasance lokacin bakin ciki a kotu yayinda wani tsohon bayarbe mai shekaru 60, Tunji Oyedele, dan kasuwa a jihar Lagas, ya bayyana cewa yana so a kashe auransa mai shekaru 22 saboda ya kama matarsa a kan gado tare da fasto dinta.

Al’amarin ya faru ne a ranar Laraba, 25 ga watan Janairu, a kotun Igando, a cikin wadanda suka je sun hada da matarsa mai shekaru 55 da kuma dan kasuwa, wanda ya zargi mutumin da lalata.

Na kama matata tare da fasto dinta a kan gado – tsoho mai shekaru 60 ya fada ma kotu
Ba hoton gaskiya ba

Oyedele yace: “A duk lokacin da nayi tafiya, matata na kawo maza gidanmu; sau biyu, ina kama matata da samarinta a dakin baccinmu. Na farko, na dawo gida ba tare da na fada mat aba kuma sai na kama ta tare da wani a dakin baccinmu. Na biyu, Na kama ta tare da wani mutumi da tayi ikirarin cewa fasto dinta ne. tayi ikirarin cewa fasto din yaso kaita wani kogi don yi mata wanka na musamman don kare ta daga harin boye.”

KU KARANTA KUMA: ‘Yata da mijina suna da wata alaka, kuma bazan iya dakatar da shi ba – wata mata ta koka

Mutumin yaci gaba da zargin cewa matarsa yar asiri ce kuma a koda yaushe tana dauke da kayan asiri dabn-daban.

Oyedele ya gabatar da hotunan kayan tsubbun, kuma ya roki kotu da ta kashe auran kamar yadda baya soyayya kuma.

A bangarenta, Romoke, ta karyata zargin ta kuma bayyana cewa suna zaune lafiya da mijinta har sai watan Janairu 2016, lokacin da ya auri sabuwar mata.

Romoke: “Bamu taba fada da mijina ba, amma da zaran lokacin da ya auri wata mata, halayensa ya chanja. Amaryarsa ta zarge ni da aika mata masu kisa kuma mijina ya mayar dani jakar dambe. Mutumin da mijina ya ganmu tare da dakin baccinmu dan ajinmu ne a makarantar firamare. Dayan mutumin kuma fasto dina ne, wanda yazo don aikin boye."

Tace bata shirya rabuwa da mijinta ba saboda tana son sa har yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng