Kowa da abin da ya dame sa: Amurka za ta aika Dalibai Duniyar wata
– Kasar Amurka na shirin aika Dalabai zuwa duniyar wata
– Za ayi kokarin girka giya a cikin wata idan an je
– Donald Trump kuma ya fara shirin gina katangar karfe
Kasar Amurka na shirin aika Dalibai zuwa Duniyar wata domin su girka giya kamar dai yadda muka samu labarai daga Birnin Los Angeles na Kasar Amurka. Wannan ne dai karo na farko a tarihi da Amurka tayi irin wannan abu.
Daliban Jami’ar California da ke Garin San Diego suna cikin wata gasar zuwa Duniya wata. Zuwa karshen wannan shekarar dai za a aika jirgi zuwa sararain samaniya inda zai je Duniyar wata.
KU KARANTA: Rikicin Gambia ya lafa
Saboda bincike dai Daliban za su yo kokarin girka giya a saman watan domin ganin yadda abubuwa suke gudana a Duniyar. Wannan dalibai suna daga cikin Dalibai sama da 3000 da aka zaba domin su je Duniyar wata. An dai zabi Dalibai 25 ne kacal a Gasar.
An dai nada sabon shugaban Kasar Amurka, Donald Trump a matsayin Shugaban Kasa na 45 a Tarihi. Tuni dai ya fara shirin gina katangar karfe tsakanin Kasar Amurka da makwabta Mexico.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook
https://www.facebook.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng