An kona gidaje 50 a jihar Taraba sakamakon rikicin kabilanci
Sama da gidaje hamsin aka kona yayin da rikicin kabilanci ya barke tsakanin wasu al’ummomi guda biyu makwabtan juna dake karamar hukumar Sardauna, na jihar Taraba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito sama da mutane 300 ne suka yi gudun hijira bayan ballewar rikicin a daren Lahadin data gabata 22 ga watan Janairu.
Kaakain rundunar yansandan jihar DSP David Misal ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace rikicin ya auku ne a tsakanin al’ummar Wuro Dande da Wuro Baba Bagura dake kusa da kauyen Tamviya a kan tsibirin Mambilla.
KU KARANTA:Mata sun yaba ma hukumar soji Najeriya kan nasarar kawo karshen yan Boko Haram
Misal yace abinda ya tunzura rikicin shine wani kara da al’ummomin suka kai wasu matasan kauyen Tamviya kotu kan zargin kai musu hari da kwace musu gari. DSP Misal yace a ranar 18 ga watan Janairu da aka saurari karar a gaban wata kotu dake garin Gembu, sai alkalin kotun ya sanya aka kama wasu daga cikin wadanda ake kara, amma sai yan kauyensu suka nuna rashin amincewarsu.
Sanadiyar haka ne yan kauyen Timviya suka diran a kauyukan Wuro Dande da Wuro Baba Bagura, inda suka kona sama da gidaje 50 kurmus. Sai dai an kama mutane 6 inji DSP Misal, sa’annan ya kara da cewa a yanzu an aika da karin jami’an tsaro yankin don tabbatar da zaman lafiya, kuma za’a cigaba da gudanar da bincike.
Yayin dayake tsokaci kan harin, shugaban riko na karamar hukumar Sardauna Stephen Nyavo yayi Allah wadai da faruwar lamarin, inda yayi kira ga al’ummomin dasu rungumi zaman lafiya da juna. Shugaban yace akwai sama da mutane 200 wadanda yawancinsu yara ne da mata dake gudun hijira a yanzu, kuma karamar hukumar ta tallafa musu da kayayyakin masarufi daban daban.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng