Rahama Sadau ta yada hotunan hutun iyalanta a Makkah

Rahama Sadau ta yada hotunan hutun iyalanta a Makkah

Bayan korarta daga Kannywood, Rahama Sadau ta samu ci gaba sosai a rayuwar ta.

Rahama Sadau ta yada hotunan hutun iyalanta a Makkah
Rahama Sadau

A yanzu haka taje hutu tare da yan’uwanta kuma ta yada kyawawan hotuna daga chan inda take a garin Makkah tare da masoyanta a shafin zumunta.

KU KARANTA KUMA: Akwai jita-jita cewa Rahama Sadau zata dawo Kannywood

A daya daga cikin hotunan, Rahama ta rubuta, ‘An karbo daga Adiyy ibn Hatim (Allah ya yarda da shi), yace: Ina tare da manzon Allah (Allah ya kara tsira da aminci a gare shi) sai wasu mutane biyu suka zo gare shi: daya daga cikin su na korafin talauci, yayinda dayan ke korafi a kan fashi. Manzo Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: A kan na fashi, zai kasance amma na dan wani lokaci kafin wani ayari zasu iya fita daga Makkah ba tare da mai tsaro ba.

A kan talauci, lokaci (Ranar kiyama) ba zai zo ba kafin daya daga cikinku ya riki Ubangijinsa sadaka kusa ba tare da gano wani ya yarda da shi daga gare shi ba. Sa'an nan (1) ɗaya daga cikinku, lalle zai tsaya a gaban Allah, zai kasance babu dogon zance tsakanin shi da shi, kuma ba wani mai fassara da zaiyi fassara gare Shi. Sa'an nan Ya ce masa: Ashe ban zo muku da dukiya ba? Kuma ya ce: Haka ne. Sa'an nan Ya ce: Shin, ban aiko maku da manzo ba? Kuma ya ce: Haka ne. Sai ya tsinkaya, ta damansa, ba zai ga komai ba face wuta, sai ya duba zuwa ga hagu kuma ba zai ga komai ba face wuta, saboda haka ko wannenku ya kare kanshi daga wuta, koda da rabin dabino ne- kuma idan babu to da magana mai dadi.(1) watau a kan lokaci. al-Bukhari ne ya ruwaito.#JumaatMubarak

KU KARANTA KUMA: Kyawawan hotunan Rahama Sadau guda 9

Kalli hotunan:

Rahama Sadau ta yada hotunan hutun iyalanta a Makkah
Rahama Sadau da yan'uwanta a Makkah
Rahama Sadau ta yada hotunan hutun iyalanta a Makkah
Rahama Sadau da yan'uwanta a Makkah

A halin yanzu Rahama ta karyata cewan zata canja addini bayan an zarge ta da yin watsi da imaninta na musulma da kuma shirin komawa addinin Kirista don ta amince da tayin Hollywood gaba daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel